Yar Manya Jinin Sarauta: Hotuna Da Bidiyoyin Shagalin Kamun Diyar Sarkin Kano, Ruqayya Bayero

Yar Manya Jinin Sarauta: Hotuna Da Bidiyoyin Shagalin Kamun Diyar Sarkin Kano, Ruqayya Bayero

  • Hotunan shagalin kamun diyar sarkin Kano, Ruqayya Bayero da angonta Amir Kibiya sun kayatar da mutane
  • Kyakkyawar amarya Ruqayya ta fito shar da ita cikin shiga ta kamala irin na ‘ya’yan gidan sarauta
  • An gano ta zaune tare da mahaifinta mai martani Alhaji Aminu Bayero da kuma sauran yan uwa da kawayenta

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - Shagali ya kankama a masarautar Kano na auren Gimbiya Ruqayya Aminu Bayero da angwanta Amir Kibiya.

Tuni kyawawan bidiyoyi da hotunan shagalin kamun bikin suka yadu a shafukan soshiyal midiya.

Sarkin Kano da wasu mata
Hotuna Da Bidiyoyin Shagalin Kamun Diyar Sarkin Kano, Ruqayya Bayero Hoto: surykmata
Asali: Instagram

Kyakkyawar amarya Ruqayya ta yi shiga ta burgewa da kamala irin na ‘ya’yan gidan sarauta sanye da alkyabba.

A cikin hotunan da shafin shahararriyar MC nan ta arewa surykmata ta wallafa a Instagram, an gano amarya tare da mahaifinta da kuma sauran dangi cikin farin ciki.

Kara karanta wannan

Insha Allahu Mijina Zai Lashe Zaɓen Gwamnan Bauchi a 2023, Ministar Buhari

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daga cikin wadanda suka halarci shagalin kamun, harda mai girma uwargidar gwamnan jihar Kano, Hajiya Hafsat Umar Ganduje.

Kalli hotuna da bidiyoyin a kasa:

Jama'a sun yi martani

fasmeen_herbs_n_spices ta yi martani:

"Masha Allah ."

thenortherntherapist ta rubuta:

"Masha Allah ❤️❤️."

asmau111_ ta yi martani:

"Er manya er Sarakuna Ta Barakallah Masha Allah,Allahumma Barik."

naseernakah1 ya ce:

"Allahumma barik."

Hotunan Kafin Aure Na Kyakkyawar Diyar Sarkin Kano, Ruqayya Bayero Da Angonta Amir Kibiya

A baya mun kawo cewa, hotunan kafin aure na kyakkyawar diyar sarkin Kano, Ruqayya Aminu Ado Bayero, da angonta sun bayyana a shafukan soshiyal midiya.

Za a dai daura auren Ruqayya Bayero da angonta Amir Kibiya a ranar 2 ga watan Satumba mai zuwa.

Duk a cikin shirye-shiryen wannan babbar rana mai zuwa, masu shirin zama ma’auratan sun ware lokaci inda suka sauki kyawawan hotuna a tare.

Kara karanta wannan

Bidiyoyin: Yadda Matasa Suka Yi Ruwan Liki Harda Su Daloli A Wajen Shagalin Dinan Dan Sarkin Kano

Asali: Legit.ng

Online view pixel