Ina Samun Miliyan N2 A Sati 2: Dalibin Najeriya Da Yajin Aikin ASUU Ya Ritsa Da Shi Ya Kafa Sana’a
- Wani dalibin Najeriya ya bayyana cewa yana amfani da yajin aikin da ASUU ke yi a yanzu wajen bunkasa kowani fanni na rayuwarsa
- Baya ga samun soyayya, matashin dan Najeriya na samun miliyoyin nairori a kasuwancin da ya fara a lokacin yajin aikin
- Yan Najeriya da suka yi martani ga bidiyonsa sun bayyana cewa labarin nasararsa abun sha’awa ne yayin da suka bukaci da ya koya masu sana’a
Najeriya – Wani matashin dan Najeriya ya nuna cewa yajin aikin malaman jami’o’i na ASUU da ke gudana a yanzu haka alkhairi ne a bangarensa domin ya yi amfani da wannan damar wajen bunkasa kasuwancinsa.
A cikin wani bidiyo, mutumin ya bayyana cewa ya kafa kasuwanci a lokacin yajin aikin kuma ya fara koyon yadda ake bunkasa sana’a ta hanyar amfani da bidiyoyi.
Kudaden shiga masu ban mamaki
Don ganin kasuwancinsa ya habbaka a yanar gizo, dalibin ya bayyana cewa ya kashe jimilar N200,000 kan samawa sana’ar suna.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wannan mataki da ya dauka ya haifar da ‘ya’ya masu idanu kuma yana samun akalla naira miliyan 2 na kudaden shiga cikin makonni biyu. Ba anan kadai ya tsaya ba, ya fada tarkon soyayya sannan ya bunkasa fasaharsa kan na’urar kwamfuta a wannan lokacin.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
WHATSAPP MEMES ya ce:
“Wanda zai yi nasara zai yi nasara kawai lokaci yake dauka wasu mutane asuu ce ta rike su suke zama a gidan mahaifinsu suna cin abinci basa yin komai ku nemi aiki akwai dalili fa.”
hawlah08 ta ce:
“Dan Allah kada ka koma makaranta. Kawai ka mayar da hankali kan wannan dan uwa. Na tabbata kana farin ciki.
Sarkin Kiriniya: Yadda Karamin Yaro Ya Bi Ya Bata Wajen Da Mahaifinsa Ya Gyara, Bidiyon Ya Kayatar Da Mutane
Usman Godwin Ugbede ya ce:
“MADALLA DAN UWA CI GABA DA ZUWA SAMA.”
Annie ta ce:
"Ahha, sauran mutane na amfana daga wannan yajin aikin yayin da nake nan na zama cikakkiyar yar aiki a gidan iyayena, duk da haka na tayaka murna.”
Legit.ng ta zanta da wani dalibai don jin yadda abun yake a bangarensa tun bayan da ASUU ta tafi yajin aiki.
Wani dalibin jami’ar fasaha ta tarayya (FUT) da ya nemi a sakaya sunansa ya ce idan ta shi ne kada ma a koma makarantar don tuni ya fara sana’ar kiwo kuma babu laifi yana ganin haske a lamarin.
Ya ce:
“Ai idan ta ni ne kada ma su janye yajin aikin dama ba wani nisa nayi a harkar karatun ba balle abun ya dameni da yawa. A level 2 nake. Yanzu haka kiwon kaji nake yi kuma Alhamdulillahi akwai rufin asiri sosai a harkar.
“Ni da za a dawo da hannun agogo baya ma duk kudaden da babanmu ya zuba a harkar karatuna ce mai zan yi ya bani sun a ja jari.”
Ahmed Musa ya caccaki gwamnatin Buhari kan yajin aikin ASUU
A wani labarin, mun ji a baya cewa Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa, ya caccaki yan siyasar Najeriya kan halin ko in kula da suke nunawa a yajin aikin da malaman jami’a na ASUU ke yi.
Dan wasan kwallon kafar ya je shafinsa na Instagram a ranar Talata, 12 ga watan Yuli, don yiwa yan siyasar kasar wankin babban bargo kan tura yaransu kasashen waje domin su yi karatu yayin da tsarin ilimin kasar ke kara tabarbarewa.
Yanzu dai yajin aikin ASUU ya shiga wata na biyar, sannan babu labarin komawa makarantu domin har yanzu an kasa cimma matsaya tsakanin malaman da gwamnatin tarayya.
Asali: Legit.ng