Sarkin Kiriniya: Yadda Karamin Yaro Ya Bi Ya Bata Wajen Da Mahaifinsa Ya Gyara, Bidiyon Ya Kayatar Da Mutane

Sarkin Kiriniya: Yadda Karamin Yaro Ya Bi Ya Bata Wajen Da Mahaifinsa Ya Gyara, Bidiyon Ya Kayatar Da Mutane

  • Yunkurin wani uba na kitsa gidansa ya hadu da cikas bayan dansa mai kiriniya ya shigo sannan ya hargitsa wuri
  • Wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya ya nuna karamin yaron yana wasa da garin filawa sannan ya bade shi a kasa inda mahaifin nasa ya gama gyarawa
  • Hakan ya baiwa mabiya shafukan soshiyal midiya dariya inda suka dunga ba’a da abun amma sam bai basu mamaki ba

Bidiyon wani karamin yaro yana bada garin filawa a wajen da mahaifinsa ke gyarawa y aba mutane da dama dariya a soshiyal midiya.

Bidiyon wanda @Virally_Social ya wallafa, ya nuno wani mutumi wanda yake gab da kammala sharar falon gidansa. Kwatsam daga sama, sai ga karamin dansa ya shigo falon sannan ya fara zuzzuba garin filawa a kasan wajen.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda Magidanci Yayi Sadaukarwa, Ya Tura Matarsa Turai, Ya Zauna a Gida Uganda

Uba da yaro
Sarkin Kiriniya: Yadda Karamin Yaro Ya Bi Ya Bata Wajen Da Mahaifinsa Ya Gyara, Bidiyon Ya Kayatar Da Mutane Hoto: @Virally_Social/Twitter
Asali: Twitter

Su dukka biyun sun tsaya kallon-kallo na dan lokaci yayin da suke nazarin abun da ya faru. Mahaifin ya bi dan nasa a fusace, inda shi kuma ya tsere ciki, ganin cewa ya jefa kansa a matsala.

Kawai sai mahaifin ya hakura ya daina bin yaron. Sannan ya koma ya ci gaba da goge wajen da ya bata, ya fara sharan daga farko sai ga fitinannen yaron ya sake dawowa da ragowar garin filawan ya juye wanda ya rage a kasan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wannan karon, sai bidiyon ya zo karshe kafin masu kallo su ga ko mahaifin yaron ya yi nasarar cafke shi.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@NeoThabo ya yi martani:

"Na so yadda yaron ya tsere."

@IdentityJoy ta ce:

"Kada a damu. Bana son su kuma."

Kara karanta wannan

Bidiyo: Magidanci Ya Ki Karbar Nama Yanka 2 Da Matarsa Ta Bashi, Ya Shiga Madafi Ya Diba Da Kansa

@Rathipa_Rampedi tayi martani:

"Yara."

Abincinki Ko Dadi Babu: Karamar Yarinya Ta Yiwa Mahaifiyarta Ba’a A Bidiyo Mai Ban Dariya, Uwar Ta Yi Martani

A wani labarin, wani bidiyo mai ban dariya wanda ya yadu a soshiyal midiya ya nuno yadda wata uwa da diyarta suke yiwa junansu ba’a.

Sun shiga wani gasa yar yayi da ke yawo TikTok wanda ya bukaci mutane biyu ko fiye da haka su yi magana a kan junansu.

Da take martani game da diyar tata, sai uwar ta bayyana cewa yarinyar na da surutu kuma tana fitsarin kwance.

Asali: Legit.ng

Online view pixel