Lokuta 11 a Tarihi da Aka Dawowa Najeriya da $3.65bn da Janar Sani Abacha Ya Sata

Lokuta 11 a Tarihi da Aka Dawowa Najeriya da $3.65bn da Janar Sani Abacha Ya Sata

  • Miliyoyin Dalolin kudi sun dawo Najeriya da sunan bangare na dukiyar da aka sata a gwamnatin Marigayi Janar Sani Abacha
  • Janar Sani Abacha ya yi mulki a matsayin shugaban kasa na zamanin soja tsakanin shekarar 1999 zuwa watan Yunin 1998
  • Ana zargin Gwamnatinsa da daukar dukiyar da ta kai Dala biliyan 5 daga Baitul-mali, na kusa da Marigayin su na karyata zargin

Abuja - Wani hoto da BBC ta fitar a makon da ya wuce ya bayyana cewa $3.65bn sun dawo daga abin da ake zargin Janar Sani Abacha ya boye a kasashen ketare.

Legit.ng Hausa ta bi sahun wannan rahoto na irin Dalolin kudin da kasashen Switzerland da Amurka suka dawo da su tun daga shekarar 1999 har zuwa yau.

1. 1998

A shekarar da Sani Abacha ya rasu aka fara gano wasu fam Dala miliyan $750 daga hannun danginsa.

Kara karanta wannan

Kyawawan Hotunan Daurin Auren Wasu Yan Najeriya A Dubai Ya Yadu, Sun Yi Shaglin Bikinsu A Saukake

2. 2000

Bayan shekaru biyu sai ga shi Gwamnatin Switzerland ta dawowa Najeriya da Dala miliyan 64 da aka boye.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

3. 2002

A shekarar ne aka samu kudin da ya fi kowane yawa, Dala biliyan 1.2 daga wajen dangin tsohon shugaban kasar.

4. 2003

This Day tace a shekarar 2003, Dala miliyan 88 da kuma Dala miliyan 160 sun fito daga Jersey da Switzerland.

5. 2005

Har ila yau kasar ta Switzerland ta sake dawowa gwamnatin Najeriya da abin da ya kai fam $461.3m a 2005.

Janar Sani Abacha
Marigayi Janar Sani Abacha Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

6. 2006

Daga dai Switzerland din ne Najeriya ya karbi wasu Dala miliyan 44.1 da ake zargin Janar Abacha ya kai kasar waje.

7. 2014

Tun bayan tafiyar Olusegun Obasanjo, kudin ba su kara fitowa ba sai $227m da aka samu daga Liechtenstein a 2014.

8. 2018

A karo na biyar, Switzerland ta dawowa kasar nan da kudi, a 2018 an karbi Dala miliyan 322 na mutanen Marigayin.

Kara karanta wannan

Bidiyoyin Shagalin Dinan Kyakkyawar Diyar Sanata Sahabi

9. 2020.

Jimillar abin da Amurka ta dawowa Najeriya da shi a shekarar 2020 daga wannan kudi ya haura Dala miliyan 311.

10. 2022

Bayan ‘yan shekaru sai aka sa hannu, Kasar ta Amurkar za ta sake dawowa Najeriya da fam Dala miliyan 23.

Su wa suka taimakawa Abacha?

A baya an ji rahoto cewa a cikin wadanda suke kula da kadarori da dukiyar da Sani Abacha da iyalinsa suka sata, babu kamar Gwamna Atiku Abubakar Bagudu.

Transparency International tace iyalin Abacha da na-kusa da shi sun saci kusan $5bn tsakanin 1993 da 1998. Ana zargin akwai hannun Mohammed Abacha.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng