Wani mutum ya kashe masoyiyarsa bisa rikicin da ya barke tsakaninsu kan katin ATM

Wani mutum ya kashe masoyiyarsa bisa rikicin da ya barke tsakaninsu kan katin ATM

  • Wani rahoto ya bayyana cewa, wani mutum ya kashe masoyiyarsa saboda sabanin da suka samu tsakar dare
  • Mazauna yanki sun bayyana abin da suka sani game da kashe wata mata a takin Orhono a jihar Delta
  • An sha samun lokuta marasa dadi da ake samun sabanin da ke kai wa ga kisa tsakanin ma'aurata da abokan zama

Jihar Delta - Wani mummunan yanayi ya faru a yankin Orhono da ke Eku ta karamar hukumar Ethiope ta Gabas a jihar Delta, wani ya kashe masoyiyarsa.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, masoyan biyu na cin duniyarsu da tsinke cikin kwanciyar hankali kafin mummunan lamarin ya faru a daren Juma'a.

Duk da cewa babu cikakken bayani kan yadda lamarin ya faru, wasu mazauna yankin sun ce matar ma'aikaciyar gona ce a wata unguwa da ke kusa.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda Magidanci Yayi Sadaukarwa, Ya Tura Matarsa Turai, Ya Zauna a Gida Uganda

Yadda wani mutum ya kashe masoyiyarsa saboda katin ATM
Wani mutum ya kashe masoyiyarsa bisa rikicin da ya barke tsakaninsu kan katin ATM | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Sun ce sahibin nata ta bijiro mata ne da dare, inda ya nemi ta bashi katin ciran kudi na ATM dinta, ita kuwa ta ki ba shi hadin kai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin da ya faru cikin dare ya ruruta wutar rigima tsakaninsu, har ta kai suka kaure da fada, kamar yadda jaridar ta kawo.

A cewar majiya:

“Wasu sun ce mutumin ya naushe ta ne a gefen cikinta, nan da nan ta fadi. Wasu kuwa sun ce ya yi amfani da makami ne wajen dukanta, nan take ta fadi, ta sheka lahira.
“Da ganin mutuwarta sai muka ji mutumin yana gudu. Ba mu san dai ko ma'aurata bane. Suna dai tare. Ba ta da da tare dashi. Amma muna kyautata zaton tana da 'ya'ya a wani wurin. Ba karamar yarinya bace. Babbar mace ce.“

Kotu ta yanke wa matashin da ya kashe budurwarsa hukuncin kisa ta hanyar rataya

Kara karanta wannan

Zub da aji ne: Yadda saurai ya guji budurwarsa saboda ta kama sana'ar tallan kifi

A bangare guda, matashin saurayi ɗan shekara 35 a duniya, Badung David Dele, wanda ya yi ajalin budurwarsa ranar masoya ta duniya a shekarar 2016, zai baƙunci lahira ta hanyar rataya.

Daily Trust ta ruwaito cewa Alƙalin babbar Kotun Jos, mai shari'a Arum Ashom, shi ne ya yanke wa suarayin hukuncin kisa ranar Talata.

Mai Shari'a Ashom ya ce Kotu ta kama wanda ake zargin da aikata laifin kisan kai wanda ke ɗauke da hukuncin kisa ƙarƙashin sashi na 221 a Fenal Code, Cap 89 a kundin dokokin arewacin Najeriya 1963.

Yan Bindiga Sun Bindige Wani Soja, Sun Sace Wani Dan Kasar Waje a Kaduna

A wani labarin, rahoton da muke samu daga jaridar Daily Trust na cewa, wasu ‘yan bindiga sun farmaki wani kamfanin gona a garin Anchau na karamar hukumar Kubau a jihar Kaduna.

An ce tsagrun sun yi bindige wani soja tare da yin awon gaba da wasu jami’an kamfanin gonar mutum biyu da misalin karfe 1:30 na ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An gano gawarwakin wasu adadi na mutanen da suka mutu a benen Abuja

An tattaro cewa, daya daga cikin wadanda aka sacen wani dan kasar Zimbabwe ne da ke aiki a kamfanin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.