ASUU Ta Ki Amincewa da N10,000 da Iyayen Dalibai Za Su Tara Don Su Janye Aiki

ASUU Ta Ki Amincewa da N10,000 da Iyayen Dalibai Za Su Tara Don Su Janye Aiki

  • Kungiyar malaman jami'a sun yi martani game da yunkurin iyayen dalibai na tara kudade domin ba malaman
  • A baya iyayen dalibai sun nemi a basu damar tara kudi domin kawo karshen yajin aikin ASUU na watanni
  • Ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin ASUU da gwamnatin Buhari tun bayan barkewar yajin aikin malaman jami'a

Najeriya - Kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) ta yi watsi da shawarin iyayen daliban jami'a na hada N10,00 kowannensu domin kawo karshen yajin da kungiyar ke yi na tsawon watanni.

Kungiyar malaman jami'a a Najeriya ta shiga yajin aiki tun ranar 14 ga watan Fabrairu, lamarin da yasa har yanzu jami'o'in kasar ke garmaka.

A ranar Laraba 24 ga watan Agusta, rahotanni sun bayyana yadda kungiyar iyayen dalibai ta kasa (NPTA) ta kawo shawarin tara kudin PTA domin ba malaman na jami'a.

Kara karanta wannan

Daga karshe: NNPP ta yi magana game da yiwuwar hadewar Kwankwaso da Tinubu a 2023

Yadda ASUU ta ki amincewa da tayin iyayen dalibai
ASUU Ta Ki Amincewa da N10,000 da Iyayen Dalibai Za Su Tara Don Su Janye Aiki | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, iyayen sun mika wasika ga ma'aikatar ilimi, inda ta bayyana shirin karbar N10,000 daga hannun iyaye domin dinke wannan baraka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Martanin ASUU

Sai dai, da take martani ga yunkurin iyaye, ASUU ta ce wannan ba daidai bane, kuma kamata yayi iyayen sun hada kai da ita wajen tursasa gwamnati ta biya musu bukata.

Shugaban ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke ne ya bayyana hakan a wata hira da gidan talabijin na Arise a yau Alhamis 25 ga watan Agusta.

Ya kuma bayyana cewa, bai kamata ake kiran Najeriya uwa a Afrika ba amma kasashen da ke makwabtaka da kasar su fi ta ci gaba ta fannin ilimi ba.

Shugaban ya kuma ce, bai kamata a sanya iyaye cikin wannan lamari da ke tsakanin gwamnati da ASUU ba, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Ba Zamu Zuba Ido Ba' Majalisar Dattawa Ta Tsoma Baki Kan Batun Kisan Sheikh Goni Aisami a Yobe

Kamfanin Mai Na NNPC Ya Lissafa Ayyuka 10 da Ya Yi da N2.3trn Na Mai a 2022

A wani labarin, kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC) ya ba da bahasin dalilin da ya sa har yanzu bai tura ko kobo daga kudaden cinikin mai tun farkon 2022 zuwa yanzu ba.

A jadawalin da ya fitar, NNPC ya bayyana dalla-dalla inda kukaden suka yi a cikin wani daftarin FAAC na watan Yuli a kafar yanar gizo.

Daftarin ya nuna cewa, tsakanin man dan mai da gas, NNPC ya tara kudaden da suka kai akalla Naira tiriliyan 2.38 daga watan Janairu zuwa Yunin 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel