Jami’ai Sun Karbe Motocin Tsohon Sanata Saboda Ya Gaza Biyan Bashin N50m

Jami’ai Sun Karbe Motocin Tsohon Sanata Saboda Ya Gaza Biyan Bashin N50m

  • Shekaru biyar da suka wuce aka saurari karar Oranto Petroleum Ltd vs Senator Nnamdi Emmanuel Andy Uba a gaban Alkali
  • Sanata Andy Uba karbi bashin Naira Miliyan 50 daga hannun kamfanin Oranto Petroleum Ltd, amma har yau bai biya kudin ba
  • A dalilin haka aka kai shi kotu, yanzu Alkali ya umarci a karbe dukiyar da Uba ya mallaka domin a iya biyan kamfanin hakkinsa

Abuja - Labari ya zo mana daga Sun a ranar Laraba, 24 ga watan Agusta 2022 cewa ‘yan sanda da jami’an kotu sun dura gidan Andy Uba a garin Abuja.

Jami’an tsaro da ma’aikatan sun karbe wasu motoci uku da Sanata Andy Uba ya mallaka. Hakan na zuwa ne bayan wani hukunci da Alkali ya taba yi.

Kara karanta wannan

Za Ayi Shari’a a Gaban Alkali da Shugaba Buhari da Ministoci da Jami’an Gwamnati

A shekarar 2017, Mai shari’a N. Mbonu Nwenyi ya zartar da hukunci a kan ‘dan siyasar, yayin da ya saurari kararsu a babban kotun jiha ta Anambra.

Kamar yadda muka ji, Andy Uba ya tabbatarwa Alkali N. Mbonu Nwenyi cewa ya karbi bashi mai karancin riba, don haka kotu ta bukaci ya biya kudin.

Maganar biyan bashi ta dawo

Rahoton yace a watan Mayun 2022 aka sake dauko maganar a babban birnin tarayya Abuja, aka kuma umarci 'dan siyasar ya sauke nauyin da ke kansa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A tsakiyar makon nan wani ma’aikacin kotu ya shaidawa manema labarai cewa sun je gidan Sanata Uba a Abuja domin tabbatar da hukuncin da aka yi.

Andy Uba
Andy Uba a lokacin takara Hoto: @OfficialAPCNig
Asali: UGC

Ma’aikatan da ke aikin tabbatar da hukuncin Alkali a kotun tarayya na Abuja, suka hada kai da wasu dakarun ‘yan sanda zuwa gidan tsohon gwamnan.

Kara karanta wannan

Taron NBA: Abin da Atiku, Obi suka fada, yayin da aka nemi Kwankwaso aka rasa

Uba wanda ya taba yin gwamna na tsawon kwanaki uku a jihar Anambra ya karbi bashi ne daga hannun kamfanin Oranto Petroleum Ltd, sai bai biya ba.

Shahararren mai kudin nan, Arthur Eze shi ne yake da kamfanin Oranto Petroleum Ltd masu hako mai. Eze mai shekara 73 yana cikin attajiran Najeriya.

Punch tace gidan ‘dan takaran na APC a zaben gwamnan jihar Anambra yana nan a kan titin T.Y Danjuma ne a unguwar Asokoro a birnin tarayya Abuja.

Jami’an da aka turo sun dauke wasu motoci kirar Jeep domin ganin Uba ya biya bashin.

Zaben 2023 sai Peter Obi

A makon yau mu ka rahoto Ayo Adebanjo, shugaban ‘Yan Afenifere ya bayyana abin da ya sa Southern and Middle Belt Leaders’ Forum ke tare da LP.

Kungiyar Afenifere mai kare hakkin Yarbawa tace Bola Tinubu da Atiku Abubakar ba su dace da mulki ba, ta na muradin Peter Obi ya karbi shugabanci.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya Jero Abubuwan da za su Hana Atiku Abubakar Samun Nasara a 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel