Idan Na Sauka Daga Kan Karagar Mulki, Zan Koma Mawaki Ne inji Gwamnan APC
- Gwamna Rotimi Akeredolu yace abin da yake hari da zarar ya bar kan kujerar Gwamna shi ne ya zama fitaccen mawakin coci
- Oluwarotimi Akeredolu yake cewa zai koyi amfani da fiyano domin ya rike rera wake-waken bege a matsayinsa na mai kunar Yesu
- Mai girma Gwamnan ya bayyana kansa da mai kaunar Ubangiji, ya bada labarin yadda ya fara sha’awar wake-waken kiristanci
Ondo - Mai girma gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu SAN ya bayyana sana’ar da zai kama idan ya bar gidan gwamnatin Akure.
Vanguard ta rahoto Gwamna Oluwarotimi Akeredolu yana cewa burinsa shi ne ya zama mawakin coci, wanda za a san da zaman shi a Duniya.
Rotimi Akeredolu ya bayyana wannan ne a lokacin da ya yi jawabi a wajen wani taro na ‘yan cocin Deeper Life Bible Church da aka yi a Ondo.
Gwamnan yana cikin wadanda aka gayyata suyi jawabi a wajen gangamin wannan shekarar.
Tarihin kaunar wakokin bege
‘Dan siyasar yace ya fara sauraron wani mai da’awa a Amurka ne, wanda ya cusa masa sakon kiristanci a wakokinsa, tun daga nan ya gamsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A dalilin haka, Akeredolu yace idan ya yi tsawon rai, ya bar gwamnati, zai maida hankali wajen koyon buga fiyano, ya bi sahun Ba Amurken nan.
Kamar yadda aka rahoto, Mai girma Akeredolu yace babu wata kungiya da yake kishinta kamar ta mawakan cocin da suka rera wakoki a taron.
“Ina son waka sosai, ina jin dadin mawakan Ondo. Da za su fito sai na fadawa SSG da ya zauna kusa da ni, babu wadanda nake kishi kamar su.”
“Sun rera waka da kyau, na ji dadi, kuma na tabbata ba za ku bar wannan wurin ba tare da samun mafita a kan matsalolin da kuka kawo ba.”
Cin zabe na ikon Allah ne - Gwamna
A jawabinsa, gwamnan na jihar Ondo ya yi magana a game da yadda yayi nasarar darewa kan mulki a 2017, yace galabar da ya samu ikon Ubangiji ne.
Kwararren Lauyan ya bayyana kan shi a matsayin wanda yake matukar kaunar Yesu, yace ya zama gwamna ne da taimakon Ubangiji, ba karfin kowa ba.
APC a kan mulkin kasa
Ganin an yi shekaru yana fuskantar rikicin Boko Haram a Borno, Kashim Shettima yace shi zai kula da harkar tsaro da zarar APC ta karbi mulki a 2023.
Sanata Shettima yake cewa idan suka kafa gwamnati a Mayun shekarar badi Bola Tinubu zai lura da sha’anin tattalin arziki kamar yadda ya yi a Legas.
Asali: Legit.ng