Gwamnatin Tarayya Ta Ba Da Kwangilar Tsare Layin Dogo A Abuja

Gwamnatin Tarayya Ta Ba Da Kwangilar Tsare Layin Dogo A Abuja

  • Gwamnatin tarayya ta amince da ware miliyan N718.16 domin aikin tsaron Titin Jirgin kasa dake birnin tarayya Abuja
  • Ministan Abuja, Muhammad Bello, ya ce an baiwa Kamfanoni biyu kwangilar ba da tsaro a layin dogon mai tsawon kilomita 45
  • Wannan matakin na zuwa ne biyo bayan harin da ƴan ta'adda suka kai wa jirgin ƙasa a watan Maris

Abuja - Majalisar zartarwa (FEC) ƙarƙashin jagorancin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta amince da ware miliyan N718.16m domin tsaron Titin Jirgin ƙasan Abuja da Tashoshinsa.

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Muhammad Bello, shi ne ya bayyana haka ga manema labarai jim kaɗan bayan taron FEC ranar Laraba, kamar yadda Channesl tv ta ruwaito.

Titin Jirgin ƙasa.
Gwamnatin Tarayya Ta Ba Da Kwangilar Tsare Layin Dogo A Abuja
Asali: Twitter

"A taron FEC yau, na gabatar da kundi kuma majalisa ta amince da baiwa Kamfanoni biyu masu zaman kansu Kwangilar samar da ingantaccen Tsaro ga Sufurin jiragen ƙasa na Abuja," inji Ministan.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tsohon Shugaban Shirin Sulhu Na Shugaban Ƙasa Ya Rasu

"Kamfanonin su ne; Messrs Al-Ahali Security Guards Limited da kuma Messrs Seaguard Security and Protective Company Limited. Za su yi aikin samar da Tsaro a baki ɗaya Layin dogon mai kilomita 45 da Tashohi 12."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Wannan aikin Tsaron zai ba da kariya ga muhimman abubuwan da ke kan Layin Dogon kamar fitilar sanarwa da kayayyakin sadarwa haɗi da duk sauran fitilu."
"Kamfanin Al-Ahali Security zai tsare Kilomita 27.4 na layin Dogon wanda ya kunshi tashohi 8 kan kuɗi N407,214,000 tsawon shekara biyu, yayin da Kamfanin Seaguard Securities, zai ba ɗa tsaro a kilomita 18 na Titin haɗi da Tashohi huɗu kan kuɗi N310,979,250."

Meyasa FG ta ɗauki wannan matakin?

Gwamnatin tarayya ta tashi tsaye ne biyo bayan harin da ƴan ta'adda suka kai kan titin Jirgin Kasan Abuja zuwa Kaduna, wanda ya yi sanadiyyar dakatar da sufuri, Tribune ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ya Rabu Da Ni Saboda Na Shiga Aikin Soja, Jarumar Soja Tayi Magana Kan Tsohon Saurayinta

A harin na watan Maris, Ƴan ta'addan sun ɗana bama-bamai, sannan suka farmaki fasinjojin jirgin, suka kashe wasu kuma suka yi garkuwa da wasu.

FG ta ce ba zata dawo da harkokin sufuri kan hanyar ba a yanzu, a cewar Ministan Sufuri, Muazu Sambo, dawo da zirga-zirga yanzu zai nuna rashin damuwa da iyalan waɗan da yan uwan su ke hannun yan ta'adda.

A wani labarin kuma 'Sako Daga Allah' Wani Babban Malami Ya Bayyana Sunan Wanda Zai Gaji Buhari a 2023

Wani Malami ya bayyana maganar Manzanci cewa ɗan takarar APC, Bola Tinubu, ne zai gaji shugaba Buhari a zaɓen 2023.

A shekarar 2019, Malamin Cocin ya yi hasashen shugaba Buhari zai lashe zaɓe karo na biyu, haka Sanata Omo-Agege.

Asali: Legit.ng

Online view pixel