Tsohon Shugaban Shirin Sulhun Tarayya, Farfesa Dokubo, Ya Rasu a Abuja

Tsohon Shugaban Shirin Sulhun Tarayya, Farfesa Dokubo, Ya Rasu a Abuja

  • Tsohon shugaban shirin sulhu na gwamnatin tarayya, Farfesa Charles Quaker Dokubo, ya rasu yana da shekaru 70 a duniya
  • Bayanai sun nuna cewa Farfesa Dokubo ya mutu ne a wani Asibiti da ke birnin tarayya Abuja ranar Laraba 24 ga watan Agusta 2022
  • An haifi marigayin ne a ranar 23 ga watan Maris, 1952 a garin Abonnema, yankin ƙaramar hukumar Akuku Toru a jihar Ribas

Abuja - Tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin Neja Delta kuma tsohon shugaban shirin sulhu na tarayya (PAP), Farfesa Charles Quaker Dokubo, ya rigamu gidan gaskiya.

Wasu bayanai da jaridar Vanguard ta tattaro sun nuna cewa, Farfesa Dokubo, ɗan kimanin shekara 70 a duniya, ya rasu ne a wani Asibiti da ke babban birnin tarayya Abuja ranar Laraba da daddare.

Kara karanta wannan

Rikicin Atiku da Wike: Ɗan Majalisar Tarayya Daga Ribas Ya Fallasa Wanda Suke Shirin Ya Gaji Buhari 2023

Farfesa Charles Quaker Dokubo.
Tsohon Shugaban Shirin Sulhun Tarayya, Farfesa Dokubo, Ya Rasu a Abuja Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

An haifi Marigayi Farfesan ne a garin Abonnema, yankin ƙaramar hukumar Akuku Toru a jihar Ribas dake kudancin Najeriya ranar 23 ga watan Maris, 1952.

Ya halarci makarantar Firamare da Makarantar Sankandire har ya kammala duk a mahaifarsa Abonnema, jihar Ribas.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Marigayin ya yi karatun 'A Level' a kwalejin Fasaha Huddersfield Technical College da ke West Yorkshire, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

A Shekarar 1978 zuwa 1980, Dokubo ya samu takardar shidar fara karatun Jami'a Admissiom a Jami'ar Teesside da ke Middlesbrough a ƙasar Birtaniya, inda ya karanci Kwas ɗin Tarihim zamani da siyasa a digirinsa na farko.

Ya kammala karatun digirinsa na biyu Masta Digiri a fannin ilimin zaman lafiya, daga bisani ya zarce digiri na uku a ɓangaren ilimin makami mai linzami da shawo kan yaduwarsa.

FG ta baiwa Kamfanoni aikin tsaron Layin Dogo

Kara karanta wannan

Fitaccen Jarumin Fina-Finai a Najeriya Ya Fice APC, Ya Koma Bayan Wanda Yake So Ya Gaji Buhari a 2023

A wani labarin kuma Gwamnatin Buhari Ta Baiwa Kamfanoni Biyu Kwangilar Makudan Kuɗi don Tsaron Titin Jirgin Abuja

Gwamnatin tarayya ta amince da ware miliyan N718.16 domin aikin tsaron Titin Jirgin kasa dake birnin tarayya Abuja.

Ministan Abuja, Muhammad Bello, ya ce an baiwa Kamfanoni biyu kwangilar ba da tsaro a layin dogon mai tsawon kilomita 45.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel