Kyawawan Hotuna da Bidiyo Daga Kamun Kabiru Aminu Bayero da Tsuleliyar Amaryarsa
- Shagalin bikin 'dan sarkin Kano, Kabiru Aminu Bayero, da kyakyawar amaryarsa, Aisha Ummarun Kwabo, ya fara kankama
- An fara shagalin auren ne a Sokoto inda aka fara da kamun amarya wanda babu ko shakka ya dauka kala da tsari me kyau
- A bidiyo da hotuna, an ga 'dan sarkin sanye da shigar alfarma yayin da amarya Aisha ta sha kyau iya kyau cikin kayan amaren zamani
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Sokoto - Kyawawan hotuna da bidiyoyin wurin kamun ango Kabiru Aminu Bayero da zukekiyar amaryarsa, Aisha Ummarun Kwabo sun matukar kayatar da jama'a
Biki tuni dai ya kankama inda ake hango ranar daurin aure, Juma'a, 26 ga watan Augustan 2020 a jihar Sokoto.
A daren Laraba ne aka fara da shagalin bikin auren inda kamun da aka yi ya matukar kayatarwa ganin yadda kyakyawar amaryar ta fito shar cikin shiga ta alfarma da kwalisa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A hotuna da bidiyoyin da @faashionseriesng suka wallafa a shafinsu na Instagram, an ga ango Kabiru Aminu Bayero sanye da shigar manyan mutane kuma ta alfarma.
Ya saka shadda mai lunin sararin samaniya inda aka yi masa tare da babbar riga tare da hula wacce ta matukar dacewa da kayansa.
Ita kuwa amarya Aisha Ummarun Kwabo, ta yi shiga ta riga mai bin jiki wacce launinta kan shi abun kallo ne.
Launin rigarta na hantar kare ne yayin da ta saka kallabinta wanda ya dace da shi tare da takalmi na 'yan matan zamani.
Auta ta Fito: Sabbin Bidiyoyin ado da cakarewar Noor Muhammadu Buhari
A wani labari na daban, sabbin bidiyoyin kwalliyar autar shugaban kasa Muhammadu Buhari da uwargidansa, Aisha Muhammadu Buhari, sun matukar kayatarwa.
A bidiyon da @theweddingstreet_ng suka wallafa a shafinsu na Instagram, an ga auta Noor Muhammadu Buhari ta sha ado iyakar ado.
A bidiyon farko, Noor Muhammadu Buhari ta bayyana sanye da rigar atamfa doguwa mai launikan shudi da ruwan kwai inda ta cike kwalliyarta da mayafi mai launin ruwan kwai.
Asali: Legit.ng