Auta ta Fito: Sabbin Bidiyoyin ado da cakarewar Noor Muhammadu Buhari

Auta ta Fito: Sabbin Bidiyoyin ado da cakarewar Noor Muhammadu Buhari

  • Bidiyoyin sabbin ado da kwalliyar 'yar autar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Noor Muhammadu Buhari sun dauka hankali
  • A bidiyoyin da @theweddingstreet_ng suka wallafa a Instagram, Auta Noor ta fito tsaf cikin shigar alfarma da gayu ta 'yan matan zamani
  • A daya daga cikin hotunan, ta saka atamfa mai launin ruwan kwai inda ta cike gayunta da mayafi mai launin, dayan kuwa shigar bakar riga aka yi mai bin jiki

Sabbin bidiyoyin kwalliyar autar shugaban kasa Muhammadu Buhari da uwargidansa, Aisha Muhammadu Buhari, sun matukar kayatarwa.

A bidiyon da @theweddingstreet_ng suka wallafa a shafinsu na Instagram, an ga auta Noor Muhammadu Buhari ta sha ado iyakar ado.

Noor Muhammadu Buhari
Auta ta Fito: Sabbin Bidiyoyin ado da cakarewar Noor Muhammadu Buhari. Hoto daga theweddingstreet_ng
Asali: Instagram

A bidiyon farko, Noor Muhammadu Buhari ta bayyana sanye da rigar atamfa doguwa mai launikan shudi da ruwan kwai inda ta cike kwalliyarta da mayafi mai launin ruwan kwai.

Kara karanta wannan

Harin Jirgin kasa: 'Dan Uwan Budurwar da Shugaban Yan Bindiga Ke Kokarin Aurawa Kansa Ya Koka

Babu shakka autar ta fito shar cikin wannan shigar kuma kyanta ya sake bayyana karara balle yadda daurin kallabinta ya fita cikin tsari..

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A bidiyo na biyu kuwa, matashiyar budurwar ta bayyana cikin doguwar riga mai launin baki dake bin jiki, wannan launin ya kara fito da hasken fatarta.

A wannan shigar, auta Noor Muhammadu Buhari bata sanya kallabi ba, sai dai an gyara gashin kanta wanda a bayyane yake sheki da walkiya irin na 'yan matan zamani.

Bidiyo: Yadda Matar Gwamna da Diyarsa Suka Kwashi Rawa wurin Liyafar Aure, An yi Musu Ruwan Kudi

A wani labari na daban, a cikin makon nan ne ake ta shagalin bikin auren diyar gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, Maryarm Atiku Bagudu.

Babu shakka bikin ya dauka kala kuma amarya ta dinga shiga ta alfarma irin ta amaren zamani kuma 'ya'yan masu hannu da shuni.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda Matar Gwamna da Diyarsa Suka Kwashi Rawa wurin Liyafar Aure, An yi Musu Ruwan Kudi

A daren jiya ne aka yi wata gagarumar liyafar cin abincin dare duk daga cikin shagalin auren Maryam Bagudu da angonta Ibrahim.

Asali: Legit.ng

Online view pixel