Shugaban Yarbawa Ya Yi Fatali da Tinubu, Ya Ayyana ‘Dan Takararsu na 2023

Shugaban Yarbawa Ya Yi Fatali da Tinubu, Ya Ayyana ‘Dan Takararsu na 2023

  • Shugaban Kungiyar Afenifere na kasa, ya shaida bai goyon bayan Bola Tinubu a zaben 2023 duk da cancantar ‘dan takaran na APC
  • Ayo Adebanjo yace Peter Obi mai neman shugaban kasa a jam’iyyar LP ne zabinsa saboda ya kamata Ibo su karbi shugabancin kasar
  • A cewar dattijon, kungiyar Southern and Middle Belt Leaders’ Forum (SMBLF) ba ta tare da Atiku Abubakar, Bola Tinubu ko waninsu

Abuja - Shugaban kungiyar nan ta Yarbawa ta Afenifere watau Pa Ayo Adebanjo, ya yi mubaya’a ga Peter Obi a zaben shugaban kasa da za ayi.

Daily Trust ta rahoto Ayo Adebanjo mai shekara 94 yana cewa ‘dan takaran LP ya kamata a zaba ba Atiku Abubakar ko Asiwaju Bola Tinubu ba.

Kara karanta wannan

2023: Tsohon Gwamna Ya Fadawa Atiku Abin da Zai Yi Idan Yana Son Cin Zabe

Dattijon ya bayyana cewa shugabannin kungiyar SMMBLF ta mutanen Kudu da Arewa maso tsakiyar Najeriya suna goyon bayan Peter Obi.

Adebanjo yake cewa ya kamata Obi ya zama shugaban kasar Najeriya a 2023 domin ayi wa mutanen Ibo adalci, su ma dai su karbi shugabanci.

Kamar yadda ya shaidawa jaridar, ‘dan takaran LP ne wanda ya fi dacewa da kawo gyara a kasa.

“Idan aka yi la’akari da tsarin karba-karba, abin da ya kawowa Tinubu tasgaro shi ne ‘Yan Kudu maso gabas sun yi mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban Yarbawa
Cif Ayo Adebanjo Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

‘Yan Kudu maso kudu ma sun rike shugabanci. Me zai hana ‘Yan kudu maso gabas? Ba batun tikitin Musulmi-Musulmi ba ne.
Tinubu ‘dan takara ne mai kyau wanda ya cancanta, abin da ya yi waje da shi, shi ne mun yi imani da tsarin karba-karba.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya Jero Abubuwan da za su Hana Atiku Abubakar Samun Nasara a 2023

- Ayo Adebanjo

Ko da bai cikin tafiyar Obidient, Adebanjo yace zaben Tinubu tamkar ayi loma biyu ne a tuwo, alhali ga wasu nan a gefe da ba suyi gatsa ko da daya ba.

The Eagle tace Adebanjo ya yi watsi da masu yi wa Atiku Abubakar kamfe da sunan mutanen yankin Arewa maso gabas ba su taba rike kujerar nan ba.

A ra’ayin Adebanjo, babu yadda za ayi mulki ya zauna a Arewa bayan Muhammadu Buhari ya shafe shekaru takwas yana jagoranci daga Mayun 2015.

Kawancen APC da NNPP

Dazu kun ji labari Etim Etim ya sanar da cewa manyan jam’iyyar APC sun amince su goyi bayan ‘dan takaran NNPP a zaben gwamnan Akwa Ibom.

Tun da APC ba ta ‘Dan takaran gwamna a jihar Akwa Ibom, watakila ‘Ya ‘yanta za su bi John Akpanudoedehe mai takara a NNPP mai kayan marmari.

Kara karanta wannan

2023: Dattawan Inyamurai sun zo Arewa, sun gana da Sarkin Musulmi kan batun magajin Buhari

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng