Wani Mai Adaidaita Ya Yiwa Kekensa Kwaskwarima Harda Kofofin Gilashi A Jos, Abun Ya Burge Mutane

Wani Mai Adaidaita Ya Yiwa Kekensa Kwaskwarima Harda Kofofin Gilashi A Jos, Abun Ya Burge Mutane

  • Wani direban adaidaita sahu a Jos ya yi fice bayan ya kawo wani sabon salo a sana’ar tasa
  • Maimakon barin kofofin adaidaitan a bude kamar yadda aka saba gani, sai mutumin ya kara kofofin gilashi a nasa keken
  • Hoton yadda aka kawata adaidaitan ya ja hankalin yan Najeriya inda suka jinjinawa mai keken

Plateau - Yan Najeriya na ta taya wani matukin adaidaita da ya kawata kekensa ta hanyar yi masa kwaskwarima murna.

Matashin wanda ke zaune a garin Jos, babban birnin jihar Plateau ya kara kofofi da windunan gilashi a adaidaitan shi, wanda hakan yasa ya fita daban da saura.

Adaidaita sahu
Wani Mai Adaidaita Ya Yiwa Kekensa Kwaskwarima Harda Kofofin Gilashi A Jos, Abun Ya Burge Mutane Hoto: Jos Rant Facebook Group/Bimba Jeremiah
Asali: Facebook

Shin da kansa ya kawata keken?

An saka kofofi da windunan gilashi kamar da su ya zo kuma sai hakan ya kara kayatar da adaidaitan fiye da sauran da aka saba gani.

Kara karanta wannan

Ya Rabu Dani Saboda Ina Da Muni: Hotunan Sauyawar Wata Budurwa Shekaru Bayan Saurayi Ya Guje Ta Ya Ba Da Mamaki

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai babu tabbacin ko mutumin da kansa ne ya sauya adaidaitar, amma dai kekunan da aka saba gani a Najeriya gaba daya basa zuwa da kofofin gilashi daga kamfani.

An wallafa hotunan wannan hadadden adaidaita a shafukan Facebook kamar su Inside Kaduna da Jos Rant.

Mabiya shafin Facebook sun yi martani

Jama’a sun tofa albarkacin bakunansu a kan wannan kokari da mutumin yayi. Wasu yan tsiraru sun ce abun bai burge su ba don zai iya kawo zufa, yayin da saura suka jinjina masa.

Kalli wasu daga cikin martanin a kasa:

Akinola Yusuf Lanre Clazzoneya ce:

"Hakan ba zai taba kasancewa ba a keke Maruwan Lagas, kofan nan ba zai yi kwana 2 ba, mutanen nan sam basu da hakuri."

Ezeaneche Precious ta yi martani:

"Karamin motar daukar fursunoni. Zai dace sosai da daukar shahararrun fursunoni zuwa kotu."

Kara karanta wannan

Kudi Kare Magana: Bidiyon Katafaren Gida Da Wani Matashi Ya Kera Cikin Watanni 4

Morolake Grace Ọlàolúwa ta ce:

“Idan wannan murfin gilashi ne, na yaba da fashar, amma yana da hatsari sosai idan muka duba yadda yawancin direbobinmu na Najeriya ke tukin ganganci.”

Elizabeth David ta ce:

“Abu ne mai kyau amma idan mutum ya yi tusa a cikin Keken nan baaba mutuwa ne wannan.”

Bidiyon Hazikin Dan Najeriya Yana Tallan Doya A Landan, Ya Ce Ya Tara N116k Cikin Awanni 4

A wani labarin, mun ji cewa duk a kokarin samun karin kudaden shigarsa, wani hazikin dan Najeriya ya fara tallan doya a unguwannin Landan.

A cikin wani bidiyo mai ban sha’awa, an gano mutumin tsaye a kan titi yana siyar da doyansa cike da alfahari da sana’arsa.

A cewar bidiyon, karin kudaden shigan zai taimaka masa wajen biyun haraji a Ingila inda yake da zama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng