'Yan Sanda Sun Kai Samame Sansanin Yan Bindiga a Katsina, Sun Sheke Dan Ta'adda

'Yan Sanda Sun Kai Samame Sansanin Yan Bindiga a Katsina, Sun Sheke Dan Ta'adda

  • Dakarun yan sanda sun kai samame sansanin yan bindiga a kauyen Anguwan Mai Zuma, ƙaramar hukumar Ɗanja a Katsina
  • Rundunar yan sanda ta ce yayin samamen, Jami'ai sun sheke ɗan ta'adda ɗaya, sun kwato kayan aikin su da yawa
  • Shugaban taawagar yan ta'addan, Sule Dawa, ya gudu da raunukan harsashi kuma yan sanda na bin diddiginsa

Katsina - Rundunar ƴan sanda reshen jihar Katsina ta ce dakarunta sun hallaka ɗan ta'adda a ƙauyen Anguwan Mai-Zuma, a yankin ƙaramar hukumar Ɗanja.

Jaridar The Cable ta ce an kama Infoma da ke yi wa yan ta'addan aiki lokacin da gwarazan yan sanda suka kai samame yankin.

Mai magana da yaawun rundunar yan sandan, SP Gambo Isah, ya ce an yi kazamin artabu ranar 20 ga watan Agusta, 2022 tsakanin dakarun yan sanda da yan ta'addan a wani wuri da ake kira baƙin sansani a ƙauyen.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Harbe Babban Jami'in Ɗan Sanda Har Lahira

Nasarar yan sanda a Katsina.
'Yan Sanda Sun Kai Samame Sansanin Yan Bindiga a Katsina, Sun Sheke Dan Ta'aadda Hoto: channelstv
Asali: Twitter

A cewarsa, gwarazan yan sandan sun kai samamen ne bayan samun wasu sahihan bayanan sirri kuma suka yi nasarar kakkaɓe yan ta'addan daga yankin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kakakin yan sandan ya ce bayanan da suka samu sun nuna cewa shugaban tawagar yan bindigan, Sule Dawa, ya tsere da harsasai a jikinsa.

Gambo Isa ya ce:

"Jami'ai sun kwato abubuwa kamar bingidar gargajiya, kakin sojoji, Adda, Wuka, Kwalabe, Galan din wani abu da ake zargin kayan shaye-shaye ne, Baburan Boxer biyu, Keken ɗinki, Batiran Mota da sauran su a mafakar yan ta'addan."

Rundunar yan sandan ta ƙara da cewa dakarun sun ƙara matsa kaimi da nufin cafke shugaban tawagar da sauran mayaƙansa.

Kwamishina ya yaba wa yan sanda

SP Isa ya ce kwamishinan yan sandan Katsina, Idrisu Dabban-Dauda, ya yaba da namijin kokarin jami'ai wajen ganin sun kawar da yan tada ƙayar bayan.

Kara karanta wannan

Sojoji Sun Kai Samame Haramtacciyar Kasuwar 'Yan Ta'adda, Sun Hallaka Su Da Dama a Arewa

Kwamishinan ya bukaci dakarun yan sandan ka da su yi ƙasa a guiwa har sai sun tabbatar sun magance duk wani kalan aikata manyan laifuka.

Ya kuma roki al'umama da su cigaba da baiwa hukumomin tsaro haɗin kai a yaƙi da ta'addanci da ya addabi jihar Katsina, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Wakilin Legit.ng Hausa ya ziyarci garin Ɗanja, Hedkwatar ƙaramar hukumar Ɗanja a jihar Kastina, inda mazauna garin suka tabbatar da faruwar lamarin.

Wani da ya nemi a ɓoye sunansa saboda tsaro ya ce an yi musayar wuta a yammacin Ɗanja kan tsaunuka, su kansu sun shiga tashin hankali suka fara kokarin guduwa.

"An yi musayar wuta har nan cikin Ɗanja domin mun yi gudu sosai hankalin mu ya tashi. Yan sandan sun kai samame can ƙauyen inda yan ta'adda suke, yana yamma da Ɗanja kan wasu tsaunuka."

Ya shaida wa wakilin mu cewa shugaban ƴan ta'adda daga can wani yankin ya gudo ya kafa sansani anan domin jinyar raunukan da jami'an tsaro suka masa.

Kara karanta wannan

Da Taimakon Mutanen Gari, Masu Garkuwa 18 Sun Shiga Komar Yan Sanda a Jihar Arewa

A wani labarin kuma 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Yan Uwan Ɗan takarar Gwamna a Jihar Shugaban Ƙasa

Yan bindiga sun sace wasu yan uwa ga ɗan takarar gwamna da ya nemi tikitin APC, Umar Tata, a Dutsinma, jihar Katsina.

Rahoto ya nuna cewa maharan sun farmaki garin Dutsinma, suka tafi kai tsaye zuwa gidan da ke kusa da na Tata, suka tasa mutum Shida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262