Ambaliyar Ruwa Ta Lakume Rayukan Mutum 10, Ta Raba Dubbanni da Mahallansu a Adamawa

Ambaliyar Ruwa Ta Lakume Rayukan Mutum 10, Ta Raba Dubbanni da Mahallansu a Adamawa

  • Gwamnatin jihar Adamawa ta tabbatar da mutuwar mutum 10 a wata mummunar Ambaliya da ta tashi mutanen kauyuka da dama
  • Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar ya ce sama da mutum 2,000 lamarin ya raba da gidajen su
  • Wannan na zuwa ne ƴan kwanaki kaɗan bayan NiMeT ta yi gargaɗin yuwuwar samun ambaliya a wasu jihohi

Adamawa - Gwamnatin jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutum 10 a wata mummunar ambaliyar Ruwa da ta auku sakamakon mamakon ruwan sama.

Daily Trust ta rahoto cewa mazauna yankin sun bayyana cewa Ambaliyar ta laƙume kananan kauyuka da dama a ƙaramar hukumar Girei, inda ta yi sanadin rushewar gidaje da lalacewar gonaki.

Ambaliyar ruwa a Adamawa.
Ambaliyar Ruwa Ta Lakume Rayukan Mutum 10, Ta Raba Dubbanni da Mahallansu a Adamawa Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Adamawa, (ADSEMA), Dakta Sulaiman Muhammadu, ya bayyana adadin mutanen da suka rasa muhallansu da mutum 2,538.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Harbe Hadimin Jigon APC Har Lahira a Wurin Shagalin Karin Shekara

Ya ce hukumar ba da agaji zata fara kai kayan tallafi na rage radadi zuwa yankun da lamarin ya shafa domin taimaka wa mutanen da suka rasa matsugunan su, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dr. Muhammadu ya ce har yanzun ba'a gano gawarwakin wasu mutum uku da suka nutse ba, yayin da wasu ƴan mata uku da suka jikka sanadin al'amarin, yanzu haka an sallame su daga Asibiti.

Bugu da ƙari, shugaban ADSEMA ya ce ma fi yawan mutanen da ke zaune a ƙauyen Jabi Lamba da wasu ƙauyula da ambaliyar ta mamaye sun koma rayuwa da yan uwan su a wasu garuruwan.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa a makon da ya gabata, hukumar hasashen yanayi ta ƙasa NiMet, ta yi gargaɗin cewa da yuwuwar wasu jihohi su fuskanci Ambaliyar ruwa a yan kwanakin nan.

Kara karanta wannan

'Yan Majalisu Biyu da Dubbannin Mambobin APC Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a Jihar Arewa

Jihohin sun haɗa da Sakkwato, Bayelsa, Bauchi da kuma Jigawa. A baya Jigawa ta tabbatar da mutuwar aƙalla mutum 50 sakamakon Ambaliya.

Mutane sun tarwatse a kauyuka 8 na jihar Kebbi

A wani labarin kuma Yan bindiga sun sake kai kazamin hari Garuruwa Takwas a jiha arewa, rayuka sun salwanta

Aƙalla mutum uku aka tabbatar sun rasa rayukansu bayan wasu miyagun yan bindiga sun aikata mummunan ta'addanci a ƙauyen Zagi da wasu ƙauyuka a ƙaramar hukumar Augie, jihar Kebbi.

A ruwayar hukumar Dillancin labarai ta ƙasa (NAN), harin da yan bindigan suka kai ranar Laraba ya bar mutane da dama kwance a Asibiti suna karɓan magani, yayin da aka sace wasu 15.

Asali: Legit.ng

Online view pixel