Tinubu, Kwankwaso da Tsofaffin Gwamnoni 11 da EFCC ta manta da Bincikensu a Yau

Tinubu, Kwankwaso da Tsofaffin Gwamnoni 11 da EFCC ta manta da Bincikensu a Yau

  • Akwai tsofaffin Gwamnoni fiye da 30 da hukumar EFCC ta ke bincike bisa zargin sata ko aikata wani laifi a lokacin ana ofis
  • Willie Obiano shi ne tsohon Gwamna na 31 da jami’an EFCC suka tabo babinsa, amma bakwai daga cikinsu aka kama a kotu
  • A cikin wadanda aka yi shari’a da su gwamnatin Muhammadu Buhari ta kuma yafewa Jolly Nyame da kuma Joshua Dariye

A wani rahoto na musamman da Premium Times ta fitar, Dataphyte sun kawo jerin tsofaffin gwamnonin da ake zargin EFCC tayi watsi da bincikensu:

1. Abdulaziz Yari

Bayan saukarsa daga kujerar Gwamna da shugaban NGF ne EFCC ta taso Abdulaziz Yari a gaba, har ta kai an tsare shi a Legas bisa zargin satar wasu N300b.

Kara karanta wannan

Iyayen zaman: Uba ya rufe shagon 'yarsa saboda ta ki amince a tafi da ira Italiya yawon karuwanci

Sannan ana zargin Yari yana da hannu a badakalar Ahmed Idris da aka dakatar. Tun farkon 2021 kotu ta karbe kadarorinsa, bayan nan ba a sake jin komai ba.

2. Theodore Orji

Tun 2021 aka tabbatar cewa EFCC ta na binciken Sanata Theodore Orji, aka kama tsohon gwamnan na Abia tare da ‘dansa a filin jirgin Nnamdi Azikwe.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

EFCC tana binciken Sanatan da ‘ya ‘yansa biyu - Chinedu da Ogbonna. Daga cikin zargin shi ne an rika cinye N500m na kudin tsaro, amma har yau shiru.

3. Tanko Al-Makura

A shekarar nan an ji yadda ma’aikatan EFCC suka cafke Tanko Al-Makura tare da mai dakinsa, inda suka sha tambayoyi a hedikwatar hukumar a Abuja.

An zargi Al-Makura da tura kudi zuwa wasu akawun a banki a lokacin yana gwamnan Nasarawa. Jaridar tace zuwa yanzu ba a sake dauko maganar ba.

Kara karanta wannan

Shiga siyasa: Matasa a Abuja sun kama wani Bishap, sun lakada masa dukan tsiya

4. Godswill Akpabio

Tsakanin 2007 da 2015, Godswill Akpabio ne ya rike Gwamna a Akwa Ibom. Watanni kadan da barinsa mulki sai EFCC ta fara zargin shi da taba Baitul-mali.

Magana ta lafa duk da an zargi Godswill Akpabio da laifin karkatar da N100bn da laifin yin gaba da N18bn daga kason FAAC da mallakar gidaje da kudin jiha.

Tinubu, Kwankwaso da sauransu
Wasu Tsofaffin Gwamnoni da ake bincike Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

5. Abdulfatah Ahmed

A watan Mayu ne aka damke Abdulfatah Ahmed, abin ya kai ga ya shafe kwanaki biyu a hannun EFCC. Tun da ya fito, har yau ba a ji EFCC ta kai shi kotu ba.

6. Aliyu Wamakko

Attahiru Bafarawa ne ya rubutawa EFCC takarda cewa ta binciki magajinsa a Sokoto, Aliyu Magatakarda Wamakko. Zuwa yanzu ba a dauki kwakwaran mataki ba.

7. Ali Modu Sheriff

A 2015, an taba kawo rahoton cafke Ali Modu Sheriff da zargin ya wawuri N300bn da yake kan kujerar gwamnati, da alama EFCC ta yi wasti da takardun binciken.

Kara karanta wannan

Zukekiyar Diyar Gwamna Atiku Bagudu Za Ta Shiga Daga Ciki, Kyawawan Hotunanta Da Angonta Sun Bayyana

8. Rabiu Kwankwaso

Tsofaffin ma’aikata sun yi ta kai korafi a kan tsohon gwamnan kan zargin taba kudin fansho, inda aka yi amfani da N10bn wajen gina wasu gidaje a jihar Kano.

Legit.ng ta samu labari Kwankwaso ya je gaban EFCC domin ya wanke kan shi. Rahoton yace babu mamaki hukumar ta sake dauko wannan shari’a a 2022.

9. Willie Obiano

Da ya bar gadon mulki, EFCC ta yi ram da Willie Obiano da sunan ya tsoma hannu a baibul mali. Tun lokacin ba a ji EFCC ta na karar Obiano a gaban kuliya ba.

10. Bukola Saraki

Tun a lokacin Ibrahim Magu aka san EFCC ta na binciken Bukola Saraki wanda ya yi shekaru 16 a kujerar Gwamnan jihar Kwara da majalisar dattawan kasar.

Daga baya aka ji hukumar yaki da rashin gaskiyar ta na binciken kudin da Saraki ya samu daga asusun jihar Kwara. Iyakar maganar kenan, ba a karasa kotu ba.

Kara karanta wannan

Karon Farko a Tarihi, Buhari Ya Kirkiro Sabon Mukami Domin Magance Rashin Tsaro

11. Bola Tinubu

A wata hira da aka taba yi da shi, Abdulrasheed Bawa yace EFCC ta na binciken Bola Tinubu game da gaskiyar dukiyarsa. Daga baya AGF ya musanaya hakan.

Dapo Apara ya kai korafi cewa Tinubu yana da hannu a kamfanin Alpha Beta Consulting da ke karbar haraji a Legas, zuwa yanzu gaskiya ba ta bayyana ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng