Badakalar Tinubu: EFCC ta ce tana ci gaba da bincikar shugaban APC Tinubu

Badakalar Tinubu: EFCC ta ce tana ci gaba da bincikar shugaban APC Tinubu

  • Shugaban hukumar EFCC ya bayyana cewa, har yanzu ana ci gaba da bincike kan Tinubu
  • Shugaban na EFCC ya bayyana cewa, bincike ba ya karewa a rana guda, yakan ja lokaci
  • Wani kamfanin ya shigar da kara kan Tinubu ya daina sarrafa kudaden kamfanin mai suna Alpha Beta

Shugaban Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya ce korafin tsohon gwamnan jihar Legas kuma jigo a jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, na hannun hukumar don ci gaba da bincike, Daily Trust ta ruwaito.

A wata hira ta musamman da jaridar ThisDay ta wallafa a ranar Lahadi, Bawa ya ce bincike ba ya karewa a cikin yini guda.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kira iyayen daliban kwalejin Kebbi, sai dai basu nemi fansa ba

Badakalar Tinubu: EFCC ta ce tana ci gaba da bincikar shugaban APC Tinubu
Shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa | Hoto: arise.tv
Asali: UGC

Ya ce:

“Kun yi min tambaya a baya game da kame mutane kafin bincike yanzu kuma kuna cewa me ya sa ba mu kama Tinubu ba? Me ya sa ba ku ce kawai 'a kame shi? ba'
“Ana ci gaba da bincike. Lokacin da kake bincika lamura irin haka, ba su karewa a rana guda. Dubban bincike na ci gaba, a kowace rana.

Bawa an ce ya nemi fom din bayyana kadarorin Tinubu lokacin da yake shugaban Ofishin shiyya na EFCC a jihar Legas.

An shigar da karar Tinubu don dakatar dashi daga sarrafa kudin wani kamfani

A bangare guda, wani tsohon Manajan Darakta na kamfanin Alpha Beta LLP, Mista Dapo Apara, ya shigar da kara yana neman wata babbar kotun jihar Legas da ta dakatar da Tinubu daga “sarrafa kudaden Alpha Beta.”

Mista Ebun-Olu Adegboruwa (SAN) ne ya shigar da karar a ranar Laraba a madadin Apara.

KU KARANTA: Ba zai yiwa ba: Shugaba Buhari ya ce ba ga kowane dan siyasa zai mika mulki ba

Badakala: Shugaban EFCC Ya Ci Alwashin Gurfanar da Wani Babba a Jami'iyyar APC

A wani labarin daban, Shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya sha alwashin cewa hukumar za ta sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Kalu.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Bawa ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja a ranar Alhamis, 17 ga watan Yuni.

Kalu, wanda yanzu haka dan majalisar dattijai ne, Kotun Koli ta sake shi a kan ka'idoji bayan an same shi da laifin satar biliyoyin nairori lokacin da yake gwamnan jihar Abia tsakanin 1999-2007.

Asali: Legit.ng

Online view pixel