Kamar Almara: Kyakkyawar Budurwa Ta Wallafa Sakonnin Soyayya Da Mai Gadinta Ya Tura Mata Ta WhatsApp

Kamar Almara: Kyakkyawar Budurwa Ta Wallafa Sakonnin Soyayya Da Mai Gadinta Ya Tura Mata Ta WhatsApp

  • Wata matashiyar budurwa yar Najeriya, Temitope Akinrimisi, ta wallafa sakonnin da mai gadinta ya aike mata ta WhatsApp
  • Mai gadin ya fada tarkon sonta tsamo-tsamo don haka ya fallasa mata sirrin zuciyarsa a dandalin zumuntan
  • Temitope ta ce a yanzu bata da sukuni a gida saboda bata yi tsammanin mai gadinta zai fada tarkon sonta ba

Najeriya - Wata matashiyar budurwa yar Najeriya mai suna Temitope Akinrimisi ta koka a shafin Twitter bayan mai gadinta ya fallasa irin son da yake mata.

Temitope ta ce ta cika da mamakin samun sakon soyayya a WhatsApp daga mai gadinta.

A sakonnin da ya wallafa a Twitter, mai gadin ya ce ta dade tana burge shi amma a yanzu ba zai iya ci gaba da boye sirrin a zuciyarsa ba.

Budurwa da sakonni
Kamar Almara: Kyakkyawar Budurwa Ta Wallafa Sakonnin Soyayya Da Mai Gadinta Ya Tura Mata Ta WhatsApp Hoto: Temitope Akinrimisi
Asali: Twitter

Ya roke ta a kan ta bashi dama sannan ta yi watsi da ganin cewa shi din mai gadi ne.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da take wallafa hotunan hirarsu a Twitter, Temi ta ce:

“Mai gadina ya fada mani yana sona. A yanzu bana jin ina da kariya kuma.”

Masu amfani da Twitter sun yi martani

Sai dai kuma, da suke martani ga lamarin, wasu da dama sun yaba da yadda mai gadin ya tsara rubutunsa.

Blest 2Reign ya ce:

“Idan har da kansa ya yi wannan rubutun, ki ce masa ya yi murabus, ki sama maku wani gidan sannan ki aure shi. Ba mai gadi bane. Mijinki ne. Idan aka yi masa dan kwaskwarima da basa dan dama zai zama mutum mai cikar zati. Kada ki yi watsi da batun.”

Core Whale ya rubuta:

“Wannan mutumin ya san kan lissafi. Don haka, yana da ilimi sosai. Idan ta dan zuba jari a kansa, zai bata wannan soyayya ta Gaskiya da ake nema a kodayaushe. Kalli soyayya ya gaskiya a wannan karnin. Baaba.”

Maria Aduba ta yi martani:

“Kawai Ina mamakin kokarin da yayi wajen hada wannan sakon soyayya mai cike da lobayya.”

Na Hadu Da Shi Bai Da Ko Waya: Budurwa Ta Kasance Da Saurayinta Har Ya Siya Motar Benz

A wani labarin, wata matashiyar budurwa @barbie_lucienne ta wallafa wani bidiyo da ke nuna saurayinta da ta kasance tare da shi lokacin da bai da komai.

Budurwar ta bayyana cewa a lokacin da ta fara soyayya da shi, mutumin bai da koda wayar hannu. Ya kasance talakan talak.

Bayan bidiyon ya fara tafiya, sai aka gano su tare a cikin wata dankareriyar mota kirar Mercedes Benz yayin da suka rike hannayen junansu cike da so da kauna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel