'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Yan Uwan Dan Takarar Tikitin Gwamnan Katsina a APC
- Yan bindiga sun sace wasu yan uwa ga ɗan takarar gwamna da ya nemi tikitin APC, Umar Tata, a Dutsinma, jihar Katsina
- Rahoto ya nuna cewa maharan sun farmaki garin Dutsinma, suka tafi kai tsaye zuwa gidan da ke kusa da na Tata, suka tasa mutum Shida
- Katsina na ɗaya daga jihohin arewa maso yammacin Najeriya da lamarin yan bindiga ya yi wa katutu
Katsina - Ƴan bindiga sun kai farmaki garin Dutsinma, hedkwatar ƙaramar hukumar Dutsinma a jihar Katsina, sun yi awon da aƙalla mutum Shida.
Daily Trust ta ruwaito cewa mutanen da maharan suka yi garkuwa da su, mafi yawam su yan uwan ɗan takarar gwamna a Inuwar APC, Umar Tata, ne.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa mutanen da harin ya shafa baƙi ne da suka zo ɗaura aure kusa da gidan fitaccen ɗan siyasan, wanda ya fafata neman tikitin takara a zaɓen fidda gwanin jam'iyyar APC.
Wata majiya mai ƙarfi ta shaida wa yan jarida cewa masu kwarmata wa yan bindiga bayanai sun taka rawa duba da yanayin yadda lamarin ya faru.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Wata mata da mafi yawan yayanta suka shiga hannun maharan ta kasance yar uwar ɗan siyasan (Tata) kuma yadda maharan suka tafi kai tsaye gidan suka sace matan akwai alamar tambaya ne," Inji mutumin.
Yadda lamarin ya faru
Wani mazaunin Dutsinma da ya nemi a ɓoye sunansa, ya ce da farko yan ta'addan sun sace mutum Tara a Anguwar Kudu Quaters da ke cikin garin amma daga baya uku sun kuɓuta.
Mutumin ya ce:
"Da farko sun kyale wata tsohuwa saboda ba zata iya tafiya da ƙafa ba da wani ƙaramin yaro da ya nace da kuka, daga baya kuma lamarin ya ƙara muni kuma mun shiga damuwa."
Haka zalika, wani Basarake wanda bai yarda a faɗi sunansa ba, ya tabbatar da faruwar lamarin da cewa, "Yanzun muka dawo daga gidan da lamarin ya faru inda muka jajantwa iyalan su."
Wane mataki hukumar yan sanda ta ɗauka?
Kakakin hukumar yan sandan Katsina, SP Gambo Isa, bai tabbatar da lamarin ba, inda ya ce bai samu rahoto game da harin ba, amma da zaran ya bincika zai sanar da manema labarai.
Legit.ng Hausa ta tuntuɓi wani mazaunin garin Dutsinma, Yahaya Jaka, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce maharan sun yi garkuwa da mutum Tara duk mata.
A cewarsa, waɗan da yan bindigan suka yi awon gaba da su tamkar 'ya'ya ne a wurin fitaccen ɗan siyasa, Umar Tata, kuma sun je garin ne halartar sha'anin biki.
"Mutum Tara suka yi garkuwa da su kuma duk mata, sun kasance tankar ƴaƴa ne a wurin Umar Tata. Lamarin ya rutsa da su ne daga zuwa Biki."
Yayin da wakilin mu ya tambaye shi ko maharan sun nemi kuɗin fansa kawo yanzu, Jaka ya ce har yanzun shiru ne babu wani bayani daga masu garkuwa da mutanen.
A wani labarin kuma Ƙasurgumin ɗan bindiga, Bello Turji, da wasu hatsabiban ƴan ta'adda sun aje Makamai a Zamfara
Mataimakin gwamnan Zamfara, Hassan Nasiha, ya ce ƙasurgumin ɗan bindiga, Bello Turji, ya rungumi shirin zaman lafiya.
Kwamitin da gwamna Matawalle ya kafa ya zauna sulhu da kungiyoyin yan bindiga Tara a kananan hukumomi uku.
Asali: Legit.ng