Dattawan Igbo Sun Zo Arewa, Sun Gana da Sarkin Musulmi Game da Takarar Peter Obi
- Zauren tuntuba na dattawan Igbo na ci gaba da neman shawarwari domin ganin yankinsu na Kudu maso Gabas ne ya kawo shugaban Najeriya a zaben shugaban kasa na 2023 mai zuwa
- Dattawan sun fara yawon neman shawari a yanzu zuwa ga manyan shugabanni a Arewacin Najeriya domin samun goyon baya a manufarsu ta lashe zabe a 2023
- Tun tuni dama dattawan Igbo suka yanke shawarar cewa, ba su da dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 da ya wuce Peter Obi
Najeriya - Dattawan yankin Inyamurai a shiyyar Kudu maso Gabashin Najeriya da wasu jiga-jigan ‘yan siyasar yankin na kara fadada nemawa Peter Obi karbuwa a Najeriya gabanin zaben 2023.
Rahoto ya shaida cewa, a yankin Arewacin kasar, dattawan sun yi tattakin dogon zango domin ganawa da Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar koli ta harkokin addinin Islama ta Najeriya, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar.
Jaridar Punch ta rahoto cewa, wannan batu na ganawar Sarkin Musulmi da dattawan Igbo na zuwa ne daga bakin sakatare janar na zauren tuntuba ta dattawan Igbo, Farfesa Charles Nwekeaku a wata hira.
A cewarsa, jam’iyyar PDP ta ci amanar kabilar Igbo, don haka kabilar ta sake tunani da marawa jam'iyyar Laboru da dan takararta baya a zaben na 2023 mai zuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Saboda haka, Farfesa Charles ya ce, kabilar na neman goyon bayan shugabannin Arewa kasancewar Obi ya samu karbuwa tun tuni a tsakanin al'ummar Arewa.
Kalamansa:
“Dole kun karanta inda (Ango) Abdullahi, shugaban zauren dattawan Arewa ya ce ba sa goyon bayan tafiyar jam’iyyun APC da PDP. Dole kun karanta hakan.
“Mun tuntube su; har yanzu muna kan tuntubarsu. Mun kai ziyara ga Sarkin Musulmi. Ina ma daga cikin tawagar da ta gana dashi. Don haka, ina magana ne cikin sani na.
“Duk wani dan Najeriya, dan Najeriya mai son cigaba a yau, yana son ganin canji. Wannan canjin dai yana hannun Peter Obi na jam'iyyar Labour.
"Don haka zauren tuntuban dattawan Igbo na nan na aiki tukuru, wajen tuntuba, ba wai ga Obi ba, ga kabilar Igbo baki daya.”
Tawagar Gwamna Wike da Ta Atiku Sun Shigawa Ganawar Sirri Don Neman Sulhu
A wani labarin, daga karshe dai sashen gwamnan Ribas Nyesom Wike da na dan takarar shugaban kasan jam’iyyar PDP mai adawa, Atiku Abubakar sun gana a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas domin dinke baraka.
A cewar rahoton jaridar The Nation, ganawar ta samu halartar gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri a matsayin jagoran tawagar Atiku da, inda suka dira fadar gwamna Wike a madadin Atiku.
Tun bayan kammala zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP na dan takarar shugaban kasa Wike da Atiku ke zaman doya da manja saboda wasu mabambantan ra'ayoyi da ke tsakani.
Jerin Manyan Mukamai 15 Masu Gwabi Da El-Rufai Da APC Ta Arewa Maso Yamma Suka Nema Daga Wurin Tinubu
Asali: Legit.ng