Ku Kawar da 'Yan Ta’adda Gaba Daya, Buhari ga Hukumomin Tsaro
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyara jihar Borno, ya kuma yi kira ga samar da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas
- Buhari ya yaba da irin kokarin jami'an tsaro da masu aikin jin kai da walwala a fadin jihar Borno
- Jihar Borno na daya daga cikin jihohin da ke fama da karancin rashin tsaro sakamakon hare-haren Boko Haram da ISWAP
Maiduguri, jihar Borno - Shugaba Buhari na Najeriya yi sake yin kira ga jami'an sojin Najeriya da su kara kaimi wajen ragargazar 'yan ta'adda don tabbatar da kawar da tsageru baki daga a Najeriya.
Shugaban ya bayyana wannan umarni a birnin Maiduguri na jihar Borno yayin wata ziyara da ya kai a jiya Alhamis 18 ga watan Agusta, Channels Tv ta ruwaito.
A cikin wata sanarwa da hadimin Buhari, Femi Adesina ya fitar, Buhari ya ce:
“Ina matukar farin ciki da irin jajircewar kwaraza kuma jami’an rundunar Operation Lafiya Dole, sauran jami’an tsaro da kuma rundunar hadin gwiwa ta MNJTFganin yadda suke yakar 'yan tada kayar baya."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Ina yaba irin kwarewarsu da yadda ragargazar maboyar ‘yan ta’adda, wanda ya kai ga inganta yanayin tsaro a wannan yanki na Arewa maso Gabas, in ba don haka ba ba zai yi wuya a samu matsugunar ‘yan gudun hijira.
“Saboda haka, ina kira da kada ku yi kasa a gwiwa, ku ci gaba da kusa kai ga maboyarsu, ku tabbatar kun kawar da su gaba daya.
“Ina kuma kira gareku da ku samar da isasshen tsaro ga manoma a harkarsu ta noma. Ana bukatar noma domin daidaito da raya yankunan karkara kuma hakan ba zai samu ba har sai an samu wadataccen tsaro ga rayukan manoma."
Hakazalika, Buhari ya umarci ma’aikatar jin kai da walwala hadi da hukumominta da su tabbatar da komowar ‘yan gudun hijira ga matsunansu ba tare da wata tsangwama ba, rahoton TheCable.
Ya kuma yaba da jajircewarsu da kuma himmatuwa da suke wajen taimakawa 'yan uwansu mutane da ke cikin bukata da tasananin hadari.
Tashin Hankali Yayin Da ’Yan ISWAP Suka Sace Manoma 6 a Jihar Borno
A wani labarin, labari mara dadi da muke samu ya bayyana cewa, wasu 'yan ta'adda da ake zargin 'yan ISWAP ne sun sace akalla manoma shida a jihar Borno.
Rahoton jaridar Daily Trust ya ce, an sace manoman ne a karamar hukumar Mafa da ke jihar Borno a Arewa maso Mabashin Najeriya a ranar Laraba 17 ga watan Agusta.
Wani fitaccen mai sharhi ga harkokin tsaro a tafkin Chadi, Zagozola Makama, ya bayyana yadda lamarin ya faru.
Asali: Legit.ng