Bidiyoyi Da Hotunan Shagalin Kamun Auren Kyakkyawar Diyar Gwamna Atiku Bagudu
- Ana shagalin bikin Maryam, diyar gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu da angonta Ibrahim Gwandu
- Bidiyoyi da hotunan bikin sun bayyana a shafukan soshiyal midiya inda amarya da ango suka fito shar dasu gwanin sha'awa
- Matar marigayi tsohon shugaban kasa, Hajiya Maryam Sani Abacha ma ta halarci shagalin kamu da aka yi na bikin
Kebbi - Shagali ya kankama sosai a gidan Gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Atiku Bagudu, na auren kyakkyawar diyarsa Maryam Bagudu.
An dai kulla aure ne tsakanin Maryam da hadadden angontamai suna Ibrahim Gwandu.
Duk a cikin shagalin bikin, an gudanar da kasaitaccen bikin Kamu na al’ada wanda ya samu halartan yan uwa da abokan arziki.

Asali: Instagram
Daga cikin wadanda suka halarci bikin Kamun harda matar tsohon shugaban kasa, Hajiya Maryam Sani Abacha.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A daya daga cikin bidiyoyin bikin da ya yadu a soshiyal midiya, an gano amarya da angon durkushe a gaban Maryam Abacha suna kwasar gaisuwa yayin da ita kuma ta sanya masu albarka.
Hakazalika an gano amarya Maryam da kawayenta suna kwasar rawa yayin da sautin kida ke tashi a dakin taron.
Amarya dai ta sanya kayan alfarma har kala biyu na rigar saki irin wadanda amare ke yayi a yanzu yayin da shi kuma ango Ibrahim ya saka shadda dinkin babbar riga.
Kalli bidiyoyi da hotunan a kasa:
Har Yanzu Sabo Fil Nake: Bidiyon Tsoho Dan Shekaru 90 Wanda Bai Taba Yin Budurwa Ko Mata Ba
A wani labarin, wani tsoho dan shekaru 90 mai suna Baizirre Jean Marie ya bayyana cewa har yanzu a kasuwa yake baida aure.
Kafar labarai ta Afrimax English ta ziyarci kauyen mutumin kuma sun zanta da shi, inda ya bayyana matsayinsa a soyayya.

Kara karanta wannan
Zukekiyar Diyar Gwamna Atiku Bagudu Za Ta Shiga Daga Ciki, Kyawawan Hotunanta Da Angonta Sun Bayyana
Baizire ya bayyanawa kafar labaran cewa ya tsaya ne a aji biyar na makarantar firamare, wanda yace bai tsinana masa komai ba.
Asali: Legit.ng