Kada Ku Zabi Dan Siyasar Da ’Ya’yansa Ke Karatu a Waje, Inji Shugaban ASUU

Kada Ku Zabi Dan Siyasar Da ’Ya’yansa Ke Karatu a Waje, Inji Shugaban ASUU

  • Shugaban kungiyar ASUU ya ba daliban Najeriya shawari kyauta, ya ce su rike katin zabensu da karfi sosai
  • Shugaban ya ce, kada dalibai su zabi dan siyasar da ke da 'ya'yan da ke karatu a kasashen waje saboda wasu dalilai
  • Kungiyar malaman jami'a sun shafe kwanaki akalla 184 suna yajin aiki saboda gwamnati ta gaza biyan bukatunsu

Najeriya - Shugaban kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) Farfesa Emmanuel Osodeke, a ranar Laraba ya shawarci daliban Najeriya kada su zabi ‘yan siyasar da ‘ya’yansu ke karatu a makarantun kasashen waje, Punch ta ruwaito.

Osodeke ya yi magana ne a shafin Twitter Space Webinar, wanda Premium Times ta shirya mai taken,‘ASUU strike, Revitalisation Fund and the Way Forward’ don nemo mafita ga mafitan yajin ASUU.

Kara karanta wannan

Ba Za a Bude Jami’o’i Kwanan nan ba, ASUU Tayi Magana Kan Dogon Yajin-Aikinta

Da yake magana kan wasu hanyoyin ci gaba na mafita ga yajin aikin, ya ce kada dalibai su zabi ‘yan siyasar da ba za su wakilci muradunsu ba.

Shugaban ASUU ga dalibai: Kada ku zabi 'yan siyasa masu 'ya'ya a kasar waje
Shugaban ASUU ya bukaci daliban Najeriya su guje 'yan siyasa masu 'ya'ya a waje | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Osodeke ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Duk wanda kuka yi imani ba zai iya biyan bukatunku ba, wanda ‘ya’yansa ke morewa da karatu a kasashen waje, wadanda ke zaune a kasashen waje, kada ku zabe su, ina kara maimaitawa, ba ku bukatar ku zabe su, domin ba ku bukatar zabar mutanen da za su kashe ku."

Osodeke yana mayar da martani ne ga tambayar da wani fitacciyar yar gwagwarmayar ENDSARS, Rinu Oduala, tayi masakan abin da daliban Najeriya za su iya yi a yunkurin karkato hankalin gwamnati ga yajin aikin ASUU.

Idan baku manta ba, malaman jami'a a Najeriya sun shiga yajin aikin tun ranar 14 ga watan Fabrairu saboda wasu matsaloli da suka gabatarwa gwamnatin Najeriya ta kuma gaza biya musu.

Kara karanta wannan

Babu haske: An kammala ganawar gwamnatin Buhari da ASUU, sakamako bai yi dadi ba

A jiya Talata ne kungiyar ta sake zama wakilan gwamnati domin jin hanyiyin da za su kawo mafita ga karewar yajin aikin kana dalibai su koma karatu.

Da yake jawabi, shugaban kungiyar ya koka da kalaman gwamnan jihar Ebonyi kuma shugaban kungiyar gwamnonin Kudu maso Gabas, David Umahi, cewa ilimin jami'a bai zama dole ga kowa ba.

Hakazalika, gwamnan ya ce babu hankali a ce gwamnatin Buhari ta ci rancen sama da naira tiriliyan daya domin biyan bukatun kungiyar malaman jami’o’i, rahoton Ripples Nigeria.

Da yake karin haske a shafinsa na Twitter, Osodeke ya ce:

“Ilimi ya shafi rayuwa. Wani gwamna yana cewa ilimi ba na kowa bane sai muka ga dansa yana kammala karatu a waje tare da gwamnoni a gefensa.
“Zan maimaita, daliban Najeriya su rike PVC dinsu da kyau, duk wanda ba zai dubi bukatunsa ba, wanda a yakin neman zabensa ba zai nuna cewa zai inganta tsarin ilimin Najeriya ba, to kada su zabe shi.

Kara karanta wannan

Shawari kyauta: Hanyoyi 15 da za ku bi domin kiyaye kanku daga fadawa matsala a Najeriya

Ganawar ASUU da FG Ta Kammala, Ba a Cimma Wata Matsaya Ta Kirki Ba

A tun farko, a ranar Talatar da ta gabata ne aka gana da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da gwamnatin Buhari, kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.

Wasu majiyoyin da ke da masaniya kan lamarin sun shaida cewa tawagar gwamnatin tarayya ta gana da wakilan kungiyar ASUU a hedikwatar hukumar kula da jami’o’i ta kasa ta NUC.

A cewar majiyar daga ASUU: “Ganawar da tawagar FG ta kasance karkashin jagorancin Farfesa Nimi Briggs kuma an fara da karfe 12:00 na rana, an kammala da karfe 3:00 na rana. Babu wani sabon tayi a teburin, kawai dai sun roke mu mu janye yajin aikin ne.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.