'Dan Garkuwa da Mutane Ya Umarci Jami’a Ta Tara Masa N10m Ko Ya Dauke Dalibai

'Dan Garkuwa da Mutane Ya Umarci Jami’a Ta Tara Masa N10m Ko Ya Dauke Dalibai

  • Wani da ake zargi da barazanar satar mutane ya fada hannun Jami’an ‘Yan Sandan Najeriya
  • ‘Yan sanda na reshen jihar Oyo sun ce sun cafke Olarinde Adekunle bayan bincike da suka gudanar
  • Adekunle ya rubuta takarda yana cewa a biya shi N10m ko dai ya yi garkuwa da daliban jami'a

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Oyo - Jami’an ‘yan sanda na reshen jihar Oyo, sun gabatar da wani mai shekara 37 da ake zargi da barazanar zai yi garkuwa da daliban makaranta.

Daily Trust ta kawo rahoto cewa an yi ram da Olarinde Adekunle ne bisa zargin barazanar awon gaba da dalibai uku masu yin karatu a jami’a.

Kamar yadda mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Oyo, Adewale Osifeso ya fada, takardar da Adekunle ya aiko da ita, ta tada hankalin jami’ar.

Kara karanta wannan

Komai Ya Ji: Bidiyoyin Wata Zukekiyar Amarya Da Angonta Sun Haddasa Cece-kuce, Sun Hadu Matuka

Guardian tace dalibai da mazauna wannan jami’a ta kudi da ke Oyo sun kidime da jin labarin wasikar barazanar, da-dama sun shiga halin dar-dar.

Bugu da kari, tsarin karatu ya birkice tun da Bayin Allah suka ji akwai yiwuwar masu garkuwa da mutane su duro jami’ar, su sace masu karatu.

A cewar Osifeso, baya ga jami'a wannan mai shekara 37 ya aika wasika ga wani bankin da ke yankin Owode, yana mai alwashin zai duro masu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jami'an 'Yan Sanda Hoto: @ngpolice
Shugaban Jami'an 'Yan Sanda na Kasa Hoto: @ngpolice
Asali: Facebook

Jawabin Adewale Osifeso

“Wani fitinannen mai garkuwa da mutane ya aika da takardar da ya rubuta da hannu zuwa ga shugabannin wata jami’ar kudi da ke garin Oyo...
inda suka yi barazanar dauke mutum uku daga cikin daliban jami’ar idan har hukumar makarantar ba ta biya N10, 000 zuwa wani lokaci ba.

Kara karanta wannan

Ke duniya: Matashin da ya durawa kabarin mahaifiyar abokinsa ashariya ya shiga hannu

“Daga nan aka shige bincike, aka cafke mutum daya, namiji, Azeez Mufutau wanda aka rubuta lambarsa a wasikun da aka aikawa banki da makarantar.
Da aka yi wa wanda ake zargi tambayoyi, sai ya tabbatar da cewa shi ne mai lambar wayar, amma ba shi ya rubuta wannan takarda ba.”
“Binciken ya kai har aka kama wani Olarinde Adekunle, namiji mai shekara 37 wanda ya amsa cewa shi ya rubuta takardun nan a boye.”

Adekunle ya kuma fadawa jami’an tsaro cewa ya yi amfani da sunan Azeez Mufutau ne domin ya boye kansa, saboda ya yi ta’adi ba tare da an gane ba.

Matsalar tsaro a yau - Ndume

Kun karanta cewa Muhammad Ali Ndume yana da ra’ayin cewa rashin kayan fada na zamani ne ya hana ta’addanci ya zama tsohon labari a Najeriya.

Da aka yi hira da shi a shirin siyasa a wata tashar talabijin a makon jiya, Sanata Ali Ndume, ya yi magana a game da mafitar rashin sha’anin tsaro.

Kara karanta wannan

Saboda Tsaro: Ku Guji Gidajen Karuwai Da Mashaya, IGP Ya Gargadi Jami’an Yan Sanda

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng