Jerin Jihohin Najeriya 15 Da Ake Biyan Malaman Makaranta N30,000 A Matsayin Mafi Karancin Albashi
Shekaru uku bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan dokar albashi mafi karanci, malaman frimare da sakandare na jihohi 15 da birnin tarayya Abuja kawai suke morar karin albashin da aka yi na N30,000.
Kungiyar malamai ta Najeriya, NUT ce ta bayyana hakan kamar yadda The Nation ta rahoto.
Jihohin da suka aiwatar da karin albashin baki daya sune:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
- Akwa Ibom
- Ebonyi
- Edo
- Ekiti
- Jigawa
- Kano
- Katsina
- Kwara
- Lagos
- Ogun
- Ondo
- Osun
- Oyo
- Plateau
- Rivers
- FCT (Abuja).
Jihohin da gaba daya aka aiwatar da karin albashin ba
An aiwatar da karin albashin wasu yankuna a jihohin Kogi, Cross Rivers; Kaduna da Yobe sun koma biyan N18,000 a matsayin mafi karancin albashi na 2011, Business Day ta rahoto.
Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan dokar karin albashin mafi karanci na N30,000 ne a watan Afrilun 2019 bayan fafatawa da kungiyar kwadago na kasa na tsawon lokaci.
Jihohi 15 wadanda ba su aiwatar da mafi karancin albashi na N30,000 ga malaman makaranta ba
Jihohin sune:
- Abia
- Bayelsa
- Delta
- Enugu
- Nasarawa
- Adamawa
- Gombe
- Niger
- Borno
- Sokoto
- Anambra
- Imo
- Benue
- Taraba
- Zamfara
Cikakken Jerin Jihohin Najeriya 24 Inda Ma'aikata Ba Su Bin Bashin Albashi
A wai rahoton, BudgIT, wata kungiyar kare hakkin farar-hula, ta fitar da sakamakon wani bincike da ta yi a jihohin kasar inda ta nuna jihohin da ma'aikata ba su bin bashin albashi da kuma wadanda ma'aikatansu ke bin bashi na akalla wata daya ko fiye da hakan.
A rahotonsa, BudgIT ta ce nuna cewa jihohi kamar Edo, Ebonyi, Ondo da Taraba da kawo yanzu ma'aikatansu na bin bashi na wata shida da fiye da hakan.
Asali: Legit.ng