Jarumin Fim Ya Siya Gidan da Harsashi Baya Hudawa kan N1.4b, ya Daga Zai Siyar

Jarumin Fim Ya Siya Gidan da Harsashi Baya Hudawa kan N1.4b, ya Daga Zai Siyar

  • Jarumin fina-finan Amurka, Steven Seagal, attajirin mai kudi ne, kuma tsabar arzikinsa har gidan da harsashi bai iya ratsawa ya siya a Arizona, Amurka
  • Fitaccen jarumin ya siya gidan a dala miliyan 3.5 wanda yayi daidai da N1,467,270,000 a shekarar 2010, yanzu kuma ya daga yana neman mai siya a $3.55 (N1,489,250,000)
  • Gidan na da girman Acre 12, inda yake da dakunan kwana 5 da bandaki guda 5, sannan a cikin hamada yake, yayin da aka sakaya kowacce kofa da get

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Fitaccen jarumin kasar Amurka, Steven Seagal wanda ya tara dukiya mai yawan gaske da sana’arsa, ya siya wani katafaren gida wanda harsashi ba ya iya ratsawa a Arizona.

Gidan a zagaye yake da hamada da kuma korayen shukoki. An gina gidan ne musamman bisa tsarin da jarumin ya bayar.

Kara karanta wannan

Karshen alewa: Kotu ta yankewa kasurgumin dan bindiga hukuncin zaman gidan magarkama

Steven Seagal
Jarumin Fim Ya Siya Gidan da Harsashi Baya Hudawa kan N1.4b, ya Daga Zai Siyar. Hoto daga Tristar Media
Asali: Getty Images

A cikin gidan akwai dakunan kwana guda biyar, bandakuna guda biyar, bangaren kallo na musamman, katafaren falon da akwai TV gine a jikin bango da kuma wuta. Har ila yau akwai masaukin baki, bayi na musamman da kuma kwatamin wanka.

Cike da kawa aka jera duwatsu, gilas da karafa, wanda aka gyara harabar gidan musamman don hamadar da ke zagaye da gidan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Katon kwatamin wankan mai daukar hankali yana zagaye da wasu duwatsu na musamman don su kara bai wa wurin kala. Sannan akwai na’ura ta musamman don sanyaya gidan saboda zafin da ke tashi a hamada da yammaci.

A bangaren wurin cin abinci na musamman da ke gidan kuwa ba a cewa komai, akwai kicin na musamman.

Akwai manyan gareji guda uku don ajiye motoci.

Steven Seagal ya daga gidan zai siyar ne bayan kusan shekaru goma da siya. Zai siyar da gidan ne a dala miliyan 3.55 daidai da N1,489,250,000.

Kara karanta wannan

Goodluck Jonathan ya Fadakar da Mutane a kan Shugabannin da ba za a Zaba a 2023 ba

Zan iya Siyan Namiji da Kudina, In Killace shi a Gidana Kuma in Juya shi Yadda Nake so - Jarumar fim

A wani labari na daban, jarumar fina-finan Nollywood, Nkechi Blessing Sunday, ta buga kirji tare da ikirarin irin dukiyar da ta mallaka inda tace za ta iya siyan namiji, ta ajiye shi a gidanta kuma ta juya shi kamar waina a tanda.

Nkechi Blessing ta bayyana wannan ikirarin ne ta Instagram yayin da ta tattauna da dilan motoci kai tsaye, Chidi Mike CMC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel