Zan iya Siyan Namiji da Kudina, In Killace shi a Gidana Kuma in Juya shi Yadda Nake so - Jarumar fim

Zan iya Siyan Namiji da Kudina, In Killace shi a Gidana Kuma in Juya shi Yadda Nake so - Jarumar fim

  • Jarumar fina-finan kudancin Najeriya, Nkechi Blessing, tace tana da kudin siyan namiji, ta killace shi a cikin gidanta mallakinta
  • Ta bayyana cewa, ita zata dinga juya mijin kamar waina a tanda kuma auren zai kasance sai abinda take so za a dinga yi
  • Ta sanar da hakan ne yayin tattaunawar kai tsaye da aka yi da ita ta Instagram kan batun aure, da kuma tilascin yin sa ga jama'a

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jarumar fina-finan Nollywood, Nkechi Blessing Sunday, ta buga kirji tare da ikirarin irin dukiyar da ta mallaka inda tace za ta iya siyan namiji, ta ajiye shi a gidanta kuma ta juya shi kamar waina a tanda.

Nkechi Blessing ta bayyana wannan ikirarin ne ta Instagram yayin da ta tattauna da dilan motoci kai tsaye, Chidi Mike CMC.

Kara karanta wannan

Bidiyon Budurwa da Wani Sabon Salon Kitso mai Bada Mamaki Ya Janyo Cece-kuce

Nkechi Blessing
Zan iya Siyan Namiji da Kudina, In Killace shi a Gidana Kuma in Juya shi Yadda Nake so - Jarumar fim. Hoto daga Infromation Nigeria
Asali: UGC

Ta shiga tattaunawar kai tsaye wacce ta karba bakuncin mutane uku banda Chidi, inda suka yi magana kan aure da kuma ko ya zama tilas mace tayi aure.

Kamar yadda jarumar fim din tace, zai zama karkashin ikonta saboda zata ajiye shi a gidanta kuma ta dinga yanke hukuncin yadda alakar zata kasance duk kuma cike da ra'ayinta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Nkechi tace:

"Ba kowa da ya zo rayuwar nan bane yake da burin aure. Hankali kwance zan iya siyan namiji da 'yan canji na da nake da shi kuma in saka shi a gidana. Zan ce ya zauna a nan kuma zai zauna har sai nace mishi ya tashi."

Latsa nan don kallon bidiyon.

Bidiyo: Yadda na asirce mijina, babu wacce ta isa ta kwace min shi, Matar aure ta sanarwa duniya

Kara karanta wannan

Bidiyo: Kyakyawar Budurwa ta Koma Aikin Boyi-boyi a Dubai, Tayi wa Masu Zundenta Martani

A wani labari na daban, wata matar aure ta janyo maganganu a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter bayan ta fallasa boyayyen sirin dake tattare da ita.

Tace ta kulle mijinta 'dan kasar Kamaru a kwalbar tsafi, wanda hakan yasa yake mata biyayya kuma ba zai taba iya kula wata mace ba a rayuwarsa.

Matar auren bata tsaya nan ba, ta wallafa bidiyonta da mijinta mai suna Michael kuma tace saboda kwalbar tsafin da ta rufe shi a ciki ne yasa baya iya cin amanarta yayin da ita kuwa take cin tashi amanar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel