Jami'an 'yan sanda sun cafke wani da yayi wa abokiyar aikin su bugun tsiya
- Jami'an 'yan sanda sun cafke wani da yayi wa abokiyar aikin su bugun tsiya
- 'Yar sandan dai ta je ta kamo mutumin ne saboda wani laifin da ya aikata amma sai ya hauta da bugu daga bisani
Jami'an 'yan sandan Najeriya dake a garin Legas a ofishin 'yan sandan garin Itire sun sanar da samun nasarar cafke wani matashi mai suna Samson Aghedo bisa zargin sa da suke yi da lakadawa abokiyar aikin su bugun tsiya.
KU KARANTA: An kama wani malamin addini bisa zargin sata
Labaran da muka samu dai sun bayyana cewa 'yar sandan dai ta je ta kamo mutumin ne a gidan sa dake a kan titin Ola mai lamba 32 saboda wani laifin da ya aikata amma sai ya hauta da bugu daga bisani.
Legit.ng dai ta samu cewa tun farko dai mutumin ya nuna tirjiya tare da kin amincewa da kamen da 'yar sandan ta zo ta yi masa wanda yayi sanadiyyar cece-kuce da cacar baki tsakanin su kafin daga bisani ya tura ta kasa ya kuma hau ta da duka.
A wani labarin kuma, Labarin da muke samu da dumi-dumin sa na nuni ne da cewa rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Benue ta sanar da gano biyu daga cikin jami'an ta hudu da suka bace a satin da ya gabata a wani kauye da ake kira Azage dake a karamar hukumar Logo a raye.
Wannan dai na kunshe a cikin wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na rundunar mai suna ASP Moses Joel ya fitar ya kuma rabawa manema labarai a jiya da dare.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng