Cikakken Jerin Jihohin Najeriya 24 Inda Ma'aikata Ba Su Bin Bashin Albashi
BudgIT, wata kungiyar kare hakkin farar-hula, ta fitar da sakamakon wani bincike da ta yi a jihohin kasar inda ta nuna jihohin da ma'aikata ba su bin bashin albashi da kuma wadanda ma'aikatansu ke bin bashi na akalla wata daya ko fiye da hakan.
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
A rahotonsa, BudgIT ta ce nuna cewa jihohi kamar Edo, Ebonyi, Ondo da Taraba da kawo yanzu ma'aikatansu na bin bashi na wata shida da fiye da hakan.
Ga Jerin jihohin da ma'aikata ba su bin gwamnati bashi zuwa karshen watan Yulin 2022.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
- Sokoto
- Borno
- Zamfara
- Katsina
- Jigawa
- Yobe
- Kano
- Bauchi
- Gombe
- FCT, Abuja
- Kebbi
- Niger
- Kaduna
- Kwara
- Enugu
- Oyo
- Ogun
- Ekiti
- Osun
- Lagos
- Akwa
- Ibom
- Rivers
- Bayelsa
- Anambra
Wani sabon rahoto ya lissafa jihohi 12 da gwamnoninsu suka ki biyan albashin watanni a jihohinsu a lokacin da ya dace.
Rahoton da BudgIT ta fitar ya nuna cewa a jihohin, a kalla ma'aikata na bin bashin wata daya a ranar 28 ga watan Yulin 2022.
Kungiyar ta nuna rashin jin dadinta kan halin da ake barin ma'aikatan gwamnati a ciki.
BudgIT ta Fallasa Jihohi 12 Dake Rike da Albashin Ma'aikata Na Tsawon Watanni
A wani rahoton, BudgIT ta bayyana damuwarta kan yadda wasu gwamnatocin jihohi suka ki biyan albashin ma'aikata.
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, BudgIT ta sanar da hakan a wata takardar da ta fitar ranar Alhamis wacce Iyanu Fatoba yasa hannu, mataimakin shugaban yada labaran kungiyar da sadarwa.
Hukumar tace sakamakon bincikenta na albasbin 2022 na kasa ya nuna cewa a kalla jihohi 12 ne ke rike da albashin ma'aikata har zuwa 28 ga watan Yulin 2022.
Asali: Legit.ng