Kidayar 2023 Za Ta Taimaka Wa Najeriya Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro, Inji Buhari

Kidayar 2023 Za Ta Taimaka Wa Najeriya Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro, Inji Buhari

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, kidayar 2023 mai zuwa za ta kawo sauyi a fannin rashin tsaro
  • Najeriya ta yi kidayar yawan al'umma da gidajen mazauna cikinta tun shekarar 2006, kalla shekaru 16 da suka gabata
  • Najeriya na fuskantar matsanancin rashin tsaro tun bayan bayyanar kungiyar Boko Haram, shekaru sama da 10 da suka wuce

FCT, Abuja - A ranar Alhamis ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana fatansa na cewa kidayar jama’a ta 2023 za ta taimaka wajen yaki da matsalar rashin tsaro da ke addabar Najeriya.

Bayanin na Buhari ya fito ne a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya fitar, Punch ta ruwaito.

Sanarwar ta ce Buhari ya bayyana hakan ne a taron masu ruwa da tsaki na kasa kan kidayar yawan 'yan Najeriya da gidajensu na 2023 da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC: Ba yadda za a yi Buhari ya ci bashin N1.1tr don biyan bukatun ASUU

Buhari ya ce kidaya za ta kawo karshen rashin tsaro
Kidayar 2023 Za Ta Taimaka Wa Najeriya Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro, Inji Buhari | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Buhari ya jaddada cewa fasahar zamani za ta tabbatar da cewa bayanan kidayar sun fito da inganci kuma a yi amfani dasu yadda ya dace.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kamata a yi kidaya tun tuni, inji Buhari

Ya bayyana takaicin cewa ba a gudanar da kidayar al’ummar Najeriya ba bisa ka’ida a duk bayan shekaru 10 kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta ba da shawara.

An yi kidayar jama’ar Najeriya ne 2006, shekaru 16 kenan akalla da suka gabata.

Shugaba Buhari ya ce kidayar 2006 ta riga ta wargaje, wannan yasa bayanan yawan 'yan Najeriya ke da shi a ma'adar bayanai, rahoton Channels Tv.

Don haka shugaban ya bukaci goyon bayan masu ruwa da tsaki da suka hada da Gwamnatocin Jihohi, Majalisun Kananan Hukumomi, bangaren Gargajiya da Addini da sauran jama’a domin samun nasarar gudanar da ayyukan kidayar ta 2023.

Kara karanta wannan

Ka Ja Kunnen Magoya Bayan Ka, Tinubu Ya Gargadi Peter Obi Kan Yada Labaran Karya

A nasa jawabin, sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya tabbatar da kalaman na Buhari tun da farko yana mai cewa duba da yanayin karuwar yawan al’umma na 2.3% bisa dari, Najeriya za ta kasance kasa ta uku mafi yawan jama'a a duniya nan da 2050.

Abin na yi ne: Za a dauki mutane miliyan 1 aiki a 2023 domin a gano yawan 'Yan Najeriya

A shirin yin wannan kidaya, hukumar NPC ta kasa, ta ce mutane miliyan daya za a dauka aiki domin taimakawa gwamnatin tarayya a kidayar da za a yi a shekara mai zuwa.

Daily Trust ta rahoto hukumar tarayyar ta na cewa za ayi amfani da fasaha na zamani wajen aikin kidayar domin hana ‘yan siyasa da sauran manya yin coge.

Sanannen abu ne cewa ana zargin wasu su kan kara yawan mutane idan aka tashi kirga adadin yawan al’umma, ana yin haka ne domin cin ma wata manufa.

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: Yan Majalisar Dokokin Jihar Katsina Zasu Sa Labule da Gwamna da Shugaba Buhari

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.