Abin na yi ne: Za a dauki mutane miliyan 1 aiki a 2023 domin a gano yawan 'Yan Najeriya

Abin na yi ne: Za a dauki mutane miliyan 1 aiki a 2023 domin a gano yawan 'Yan Najeriya

  • Hukumar kidaya ta Najeriya ta na shirye-shiryen yadda za a kirga duka mutanen kasar nan a 2023
  • Kwamishinan NPC na jihar Ekiti ya ce mutane miliyan guda za a dauka domin su yi wannan aiki
  • Deji Ajayi ya bayyana irin shirye-shiryen da aka yi, ya ce zai yi wahala a fitar da alkaluman karya

Ekiti - Hukumar NPC ta kasa, ta ce mutane miliyan daya za a dauka aiki domin taimakawa gwamnatin tarayya a kidayar da za a yi a shekara mai zuwa.

Daily Trust ta rahoto hukumar tarayyar ta na cewa za ayi amfani da fasaha na zamani wajen aikin kidayar domin hana ‘yan siyasa da sauran manya yin coge.

Sanannen abu ne cewa ana zargin wasu su kan kara yawan mutane idan aka tashi kirga adadin yawan al’umma, ana yin haka ne domin cin ma wata manufa.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Bikin 'yancin kai ya zo da tsaiko a Amurka, 'yan bindiga sun harbe jama'a

Wannan bayani ne ya fito ne daga bakin Kwamishinan NPC mai wakiltar jihar Ekiti, Deji Ajayi.

Za ayi kidayar gwaji a wasu wurare

Da yake gabatar da jawabi a garin Ado-Ekiti a ranar Litinin, 4 ga watan Yuli 2022, Ajayi ya shaida cewa za a fara yin kidaya na gwaji domin a gane bakin zaren.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jaridar ta rahoto Ajayi yana mai cewa an ware garuruwa tara da ke cikin kananan hukumomi 16 da ake da su a jihar Ekiti, a nan za a gudanar da kidayar gwajin.

'Yan Najeriya
Mutane su na shakatawa a Legas Hoto: edition.cnn.com
Asali: UGC

Garuruwan da aka zaba su ne; Ado, Emure, Iro, Ijero, Ikole, Iworoko, Ise, Ikun da Omuo Ekiti. Idan abubuwa sun tafi daidai, sai ayi kidayar asali a shekara mai zuwa.

Muhimmancin sanin yawan al'umma

Tsohon shugaban ma’aikatan gwamnatin na jihar Ekiti ya nuna muhimmancin wannan kidaya, ya ce da alkaluman ne za a rika tsara yadda za a taimaki matasa.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: Akwatunan zabe 748 sun kone a inda tsageru suka kona ofishin INEC

Haka zalika ta haka ne za a samu adadin yadda za ta kula da matasa da dalibai, a kuma tsara yadda sauran al’umma da marasa karfi za su ci moriyar gwamnati.

Za a iya yin cuwa cuwa a kidayar 2023

A kidayar da za ayi wannan karo, kwamishinan na NPC ya ce zai yi wahala a samu wanda zai yi coge domin wannan karo an kawo na’urorin fasaha na zamani.

Hukumar ta tanadi kayan aikin da za su rika daukar fuskoki da zanen hannuwa, saboda haka za a iya fatali da duk wanda ya fito fiye da sau daya a kan na’urorin.

Babu takardar firamare

A makon baya ne aka samu rahoto Joe Anekhu Ohiani ya bayyana a gaban majalisar dattawa domin a tabbatar da shi a matsayin shugaban hukumar ICRC.

Kwamitin ayyuka a karkashin Sanata Muhammad Adamu Aliero ya fahimci Anekhu Ohiani bai da takardar gama firamare, a dalilin haka ne aka ki tabbatar da shi.

Kara karanta wannan

Hukuncin namijin da yaci amanar matarsa bisa kundin tsarin mulkin Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel