Nagode wa Najeriya da ta Bani Ilimi Nagartacce, Mai Arha: Matashin Najeriya Dake Digirin Digirgir a Amurka
- Wani matashi mai suna Ebuka Peter Ezugwu ya mika sakon godiyarsa ga Najeriya da ta bashi ingantaccen ilimi kuma mai arha
- Ebuka yana karatun digirin digirgir dinsa a fannin Injiniyanci a jami'ar Minnesota kuma yace dole ne ya godewa Najeriya
- 'Yan Najeriya masu yawa a Twitter sun amince da shi kan cewa ilimi a Najeriya arha gare shi, amma wasu sun ce babu nagarta ko kadan
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Wani dalibin Najeriya dake karatun digirinsa na uku a Amurka ya mika sakon godiyarsa gida Najeriya kan gatan da ya samu a fannin ilimi.
Kamar yadda matashin mai suna Ebuka Peter Ezeugwu ya bayyana, da ilimi mai arha kuma nagartacce na Najeriya da ya samu ne yasa har ya iya zuwa kasar waje.
Ebuka a halin yanzu yana karatun digirinsa na uku a fannin injiniyanci a jami'ar Minnesota.
Kamar yadda ya sanar a Twitter:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Nagode wa Najeriya da ta samar min da ingantaccen ilimi a farashi mai arha. Ginshikin da na samu shi ne ya shilla ni har na fara digirin digirgir a Injiniyanci a jami'ar Minnesota, kwalejin kimiyya da Injiniyanci. Za mu cigaba."
Ma'abota amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter sun yi martani.
@iyaboawokoya tace:
"Ubangiji zai shilla ka gaba da nan yarona. Nagode da kasa muke alfahari da kai. Sararin samaniya ba za ta tare nasarorinka ba. Za ka cigaba da samun nasara da sunan Yesu. Amen."
@walebalogunk yace:
"Idan ba don karatu mai arha na jami'o'in Najeriya ba da mutane irinmu suka samu, Ubangiji kadai ne ya san inda mutane irinmu zasu kada. Godiya ta tabbata ga Ubangiji."
@fawekuntoba:
"Ubangiji yayi maka albarka da ka yabawa gudumawar da kasar mu ta gado ta bai wa cigabanka kuma ina fatan Ubangiji ya dafa maka a wannan sabon matsayin da kake nema. Ameen."
@olusogaowoye yace:
"Wadanda suka yi nasara a wajen Najeriya basu tsine mata. Wadanda ke fama ne ke neman wanda zasu dorawa laifi."
Musulma ta Kammala Digiri a Jami'ar Kiristoci Matsayin Dalibar da Tafi Kowa Hazaka
A wani labari na daban, wata matashiyar budurwa 'yar Najeriya mai suna Oyeneyi Adiat, ta zama daliba mafi kwazo da ta kammala karatu a jami'ar Bowen, mallakin Kiristoci.
A wallafar da makarantar tayi a Facebook, dalibar da ta kammala digiri tace ta ga ikon Allah a fannoni daban-daban a lokacin da take dalibar jami'a.
Ta bayyana cewa, a karatun da tayi a makarantar wanda ta kwashe tsawon shekaru bakwai da watanni tara, ta samu manyan nasarori.
Asali: Legit.ng