Bidiyo: Yaro Ya Tsokani Mahaifiyarsa Mai Juna Biyu, Ta Daura Masa Kwallon Kankana Don Ya Ji Yadda Abun Yake

Bidiyo: Yaro Ya Tsokani Mahaifiyarsa Mai Juna Biyu, Ta Daura Masa Kwallon Kankana Don Ya Ji Yadda Abun Yake

  • Wata uwa mai suna Jenna Ciambotti Shaffer, ta koyawa danta hankali yayin da ta sanya shi daura kwallon kankana a cikinsa
  • Jenna ta bayyana cewa dole ta aikata hakan don yaron ya san yadda take jin nauyin jikinta yayin da take dauke da tsohon ciki
  • Mutane da dama da suka kalli bidiyon a Instagram sun jinjinawa yadda matar take tafiyar da harkokinta a matsayinta na uwa

Wata uwa mai yara uku, Jenna Ciambotti Shaffer, ta wallafa wani bidiyo na daga daga cikin yaranta dauke da kwallon kankana a kan cikinsa.

Jenna ta bayyana cewa yaron na zolayarta lokacin da take dauke da juna biyu na makonni 39 saboda bata iya tashi kai tsaye daga kan gado.

Karamin yaro
Bidiyo: Yaro Na Tsokanar Mahaifiyarsa Mai Ciki, Ta Daura Masa Kwallon Kankana Don Ya Ji Yadda Abun Yake Hoto: @jennashaf2
Asali: Instagram

Yana dauke da dan kankana

Don ta nunawa yaron yadda ake ji idan ciki ya tsufa, sai ta daura masa katon kwallon kankana a cikinsa.

Kara karanta wannan

Yan Baiwa: Bidiyon Wasu Kyawawa Yan Gida Daya Da Duk Jikinsu Gashi Ne Har Fuska

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bayan haka, sai ta sanya yaron yin wasu ayyukan da take yi a gidan, kamar su hawa saman bene, bacci a kan gado da kuma tashi. Yaron ya sha wahala sosai wajen aikata su.

Kalli bidiyon a kasa:

Legit.ng ta tattara wasu daga cikin martanin mutane a kasa:

jensen_james10 ta ce:

"Akalla ya yi kokari akai. Aikinka ya yi kyau yaro."

samskyarts ta ce:

"Zai ji tausayin mata sosai idan ya girma! Tarbiya mai kyau."

fayizashakir ta ce:

"Abun dariya, zan tuna wannan idan dana ya girma sannan ya yi mun ba'a."

kimberly.varner ta ce:

"Zai zama mijin kirki wata rana saboda wannan!"

Yadda Tsoho Dan Shekara 93 Ya Angwance Da Budurwarsa Mai Shekaru 88, Sun Hadu Ne A Soshiyal Midiya

A wani labari na daban, wata amarya da angonta sun tabbatar da wannan fadin da ake na cewa soyayya na sama da komai yayin da suka kulla auratayya a tsakaninsu duk da tsufansu.

Kara karanta wannan

Abuja Ba Na Yaku-bayi Bane: Budurwa Ta Nuna Gidan Haya Na N750,000 Da Wani Dillali Ya Kaita, Bidiyon Ya Yadu

Babu abun da ya kai samun abokin rayuwa, wanda zuciyarka ke shaukinsa tare da burin son kasancewa da shi muddin rayuwarka.

Wasu tsoffin masoya sun auri junansu, kuma sun bayyana cewa sun hadu da soyayya a daidai lokacin da basu yi tsammanin samunsa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel