Yan Baiwa: Bidiyon Wasu Kyawawa Yan Gida Daya Da Duk Jikinsu Gashi Ne Har Fuska

Yan Baiwa: Bidiyon Wasu Kyawawa Yan Gida Daya Da Duk Jikinsu Gashi Ne Har Fuska

  • Wata matashiyar budurwa wacce yan gidansu ke da gashi a duk jikinsu har fuska ta burge mutane da dama a soshiyal midiya
  • Mutane da dama sun ce hujja ta nuna sun gaji gashin ne daga mahaifiyarsu wacce ita ma haka take
  • Daga cikin wadanda suka yi martani ga bidiyon nata akwai yan TikTok wadanda suka ce kyawunsu ya fita daban a mutane

Wata matashiyar budurwa, Vicklin Watson, ta je shafukan soshiyal midiya don nuna yadda take da yawan gashi a jiki da fuskarta, wanda ta ce ta gada ne daga wajen mahaifiyarta.

Ba ita kadai ce ke da wannan baiwa ba, harma da kaninta da kanwarta duk suna da shi. Wani bidiyo da Watson ta yada a yanar gizo ya nuna yadda fuskarta ke lullube da gashi. Abun ya kai har kafadarta.

Kara karanta wannan

Abuja Ba Na Yaku-bayi Bane: Budurwa Ta Nuna Gidan Haya Na N750,000 Da Wani Dillali Ya Kaita, Bidiyon Ya Yadu

Masu gashi
Yan Baiwa: Bidiyon Wasu Kyawawa Yan Gida Daya Da Duk Jikinsu Gashi Ne Har Fuska Hoto: TikTok/@vicklinwatson
Asali: UGC

Kanwarki ta hadu

A cikin gidan nasu gaba daya, karamar kanwar Watson ta fi kowa yawan gashi a jikinta. Mutane da dama sun ce iyalinta sun fita daban kuma su din kyawawa ne.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Masu amfani da shafukan soshiyal midiya sun kara da cewar karamar kanwar ta fi kowa kyau a gidan.

Kalli bidiyon a kasa:

Legit.ng ta tattara wasu daga cikin martanin jama’a

kamathenjwa3693 ta ce:

“Ina kaunar karamar kanwarki.. ta yaya zan iya samun hotunanta.”

brittneylawrence85 ta ce:

“Ku dukka kuna da kyau kuma kun yi daban.”

user2066130718758 ta ce:

“haka muke ni da diyata.”

midnight skye ta ce:

“gaskiya na so ace nima ina karfin gwiwar da duk kuke da shi.”

Hotuna: Tsantsar Kyawun Wani Ango Da Amaryarsa Ya Sa Mutane Yamutsa Gashin Baki A Soshiyal Midiya

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Amarya Ta cafke Dalolin Da Aka Lika Mata A Wajen Liyafar Bikinta

A wani labarin, a karshen makon jiya ne aka daura auren wani kyakkyawan ango mai suna Abdul’ziz Babaji da hadaddiyar amaryarsa Aisha Aliyu Othman.

Hotunan ma’auratan ya yadu a shafukan soshiyal midiya inda suka yi shigarsu ta sabbin aure mai cike da kamala.

Sai dai tsantsar kyawu da suke da shi shine abun da ya fi jan hankalin mabiya shafukan soshiyal midiya, harma wasu na hango yadda zuri’ar da za su samu a gaba za su kasance.

Asali: Legit.ng

Online view pixel