Harin jirgin Abuja-Kaduna: Ƴan ta'adda sun sako Sadiq Ango Abdullahi, ɗan Mama Taraba

Harin jirgin Abuja-Kaduna: Ƴan ta'adda sun sako Sadiq Ango Abdullahi, ɗan Mama Taraba

  • 'Yan ta'addan da suka kai farmaki jirgin kasa da ya dauko fasinjoji daga Abuja zuwa Kaduna sun sako Sadiq Ango Abdullahi
  • An sako dan siyasan ne a ranar Juma'a bayan an biya wasu makuden kudade a matsayin kudin fansa wanda har yanzu ba a san ko nawa bane
  • Sadiq Ango Abdullahi dan takarar majalisar wakilai ne kuma dan shugaban kungiyar dattawan arewa, Farfesa Ango Abdullahi da marigayiya Sanata Aisha Jummai Alhassan

'Yan ta'addan da suka yi garkuwa da fasinjojin jiorgin kasan Abuja zuwa Kaduna a cikin watan Maris, sun sako Sadiq Ango Abdullahi, dan shugaban kungiyar dattawan arewa, Farfesa Ango Abdullahi da marigayiyar matarsa, Sanata Aisha Jummai Alhassan, wacce aka fi sani da Mama Taraba.

Vanguard ta ruwaito cewa, Sadiq ya kwashe sama da wata daya a hannun miyagun, kuma an sako shi a ranar Juma'a bayan biyan wasu makuden kudi da ba a bayyana ko nawa bane a matsayin kudin fansa ga 'yan ta'addan.

Kara karanta wannan

Na rantse babu wanda zai saci ko kwabo idan na zama shugaban kasa, Atiku

Harin jirgin Abuja-Kaduna: Ƴan ta'adda sun sako Sadiq Ango Abdullahi, ɗan Mama Taraba
Harin jirgin Abuja-Kaduna: Ƴan ta'adda sun sako Sadiq Ango Abdullahi, ɗan Mama Taraba
Asali: Original

Har yanzu 'yan sanda ba su yi tsokaci kan lamarin ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Online view pixel