Turnuku fadan Aljanu: Ana Gwabza Rikici tsakanin Dakarun Sojoji da ‘Yan Sanda

Turnuku fadan Aljanu: Ana Gwabza Rikici tsakanin Dakarun Sojoji da ‘Yan Sanda

  • ‘Yan Sanda sun fitar da jawabi kan takkadamar da aka samu da sojoji a Legas a makon jiya
  • Sojoji sun fito suna cewa wani ‘Dan sanda ne ya harbi jami’insu a lokacin da aka samu sabani
  • Amma David Hundeyin ya karyata zancen, yace haka kurum sojojin suka aukawa jami’ansu

Lagos - Rundunar ‘yan sandan Najeriya da ke Legas sun kalubalanci Sojojin kasa da su nuna hujjar da ke nuna an harbi wani soja a wajen rigima kwanaki.

Daily Trust ta rahoto Dakarun Bataliya ta 81 suna maidawa jami’an sojojin kasar nan martani.

A makon da ya wuce aka samu labari cewa sojoji sun bugi wani jami’in ‘dan sanda mai suna Monday Orukpe a Ojo, wannan ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

Sojoji sun dawo bakin aiki ne yayin da ‘dan sandan yake bada hannu a titin Legas-Badagry, sai suka fusata saboda bai ba motocinsu damar wucewa ba.

Kara karanta wannan

Yadda Dan Najeriya Ya Badda Kamanni A Matsayin Mace A Facebook, Ya Damfari Dan Indiya Naira Miliyan 31

A dalilin wannan, sojoji suka fito daga mota suka dauke jami’in, suka yi gaba da shi. Tun bayan da abin ya faru, aka samu rashin jituwa tsakanin bangarorin.

Benjamin Hundeyin ya maida raddi

A ranar Larabar nan, 10 ga watan Agusta 2022, jaridar tace kakakin ‘yan sanda na reshen jihar Legas, Benjamin Hundeyin ya fitar da wani jawabi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dakarun Sojoji da ‘Yan Sanda
Jami'an tsaron Najeriya Hoto: www.vanguardngr.com
Asali: UGC

Benjamin Hundeyin ya zargi sojoji da kokarin boye gaskiyar abin da ya faru, yace ‘yan sanda ba su yarda sojoji su murguda ainihin abin da ya wakana ba.

“Rundunar ‘yan sandan Legas sun samu labarin abin da GOC na sojoji, Janar Umar Musa ya fada na cewa ‘dan sanda ya harbi sojoji da aka samu takaddama.”
“Gaskiyar abin ya faru shi ne a ranar Laraba 3 ga watan Agusta 2022, a kasuwar Duniya, sojoji 30 sun kai wa ‘yan sanda biyar hari saboda sun tsaida su a titi.”

Kara karanta wannan

Babban kamu: Mata 7 da ke kai wa Boko Haram kayan abinci sun shiga hannu a Borno

“Sojojin sun ci zarafin jagoran ‘yan sandan, suka dauke harsashinsa, suka yi gaba da jami’ai biyu, na ukun sai ya harba bindiga a iska, sai sojoji suka yi gaba.”

Jawabin yake cewa babu wanda ‘dan sandan ya harba lokacin. Rahoton ya kuma ce ‘yan sanda sun yi ta’aziyyar rashin jami'i da addu’ar samun sauki ga sauran.

Badakalar da ke cikin PSC

An ji labari cewa an batar da N447m da sunan aikin kafinta, sannan N200m sun tafi wajen wasu kwangiloli da ba a san kan su ba a hukumar PSC ta kasar nan.

A wasikar da Naja’atu Muhammad ta aikawa EFCC, za a ji zargin facaka da dukiyar gwamnati da Shugaban hukumar kula da 'yan sanda, Musiliu Smith yake yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng