Miyagun da Sun fi Karfin ‘Yan bindiga Sun bullo, Kila a Hakura da Zabe a Yankunan Arewa

Miyagun da Sun fi Karfin ‘Yan bindiga Sun bullo, Kila a Hakura da Zabe a Yankunan Arewa

  • Abubakar Siddique Mohammed yana ganin kamar ba za a iya yin zabe a wasu bangarorin Najeriya ba
  • Shugaban cibiyar CEDDERT ya bayyana haka da ya gabatar da jawabi a gidan taro na Mambayya a Kano
  • Farfesa Mohammed yace akwai ‘yan ta’adda masu hadari da suka shigo Kaduna, Katsina da kewayensu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Fitaccen masani kuma malamin jami’a, Abubakar Siddique Mohammed yayi gargadi cewa babu mamaki ba za iya yin zabe a wasu wurare ba.

A ranar Talata, 9 ga watan Agusta 2022, Daily Trust ta rahoto Farfesa Abubakar Siddique Mohammed yana kuka da matsalar rashin tsaro a kasar nan.

Farfesa Abubakar Siddique ya bayyana cewa an samu bayyanar wata kungiya da ta fi karfin ‘yan bindigan da aka sani a wasu jihohin da ke bangaren Arewa.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: 'Yan Shi'a 6 da Jami'an Tsaro Suka Bindige a Zaria

Farfesan wanda ya yi fice wajen nazarin irin wannan matsala yake cewa ‘ya ‘yan wannan kungiya sun fara yada akidunsu a Birnin Gwari da Dandume.

Abin har ta kai ‘yan ta’addan sun fara yin karfi a wadannan garuruwa da ke Katsina da Kaduna. 'Yan wadannan kungiya sun sha bam-bam da 'yan bindiga.

Jawabin Abubakar Siddique Mohammed

“Yanzu haka wata kungiya da ta fi ‘yan bindiga hadari ta bayyana a wasu bangarorin jihohin Arewa maso yammacin kasar nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

INEC.
Malaman zabe a Osun Hoto: @inecnigeria
Asali: Twitter
Kungiyar ta karbe iko a Birnin Gwari, Dandume, da yankunan Kaduna, Katsina, Zamfara har da wasu bangarorin jihar Neja.
'Yan wannan kungiya sun fi ‘yan bindiga hadari, saboda ‘yan bindiga ba su da akida illa kashe mutane da karbar kudin fansa.
Amma wadannan mutane suna yada akidunsu. Tsoro na shi ne ba za a iya gudanar da zaben 2023 a wadannan wurare ba.”

Kara karanta wannan

Da zafi-zafi: Sojoji sun gano dan ta'addan da ya kitsa kai hari kan tawagar Buhari a Daura, sun sheke shi

An tuna da gwagwarmayar NEPU

Abubakar Siddique wanda shi ne Centre for Democratic Development Research and Training (CEDDERT) da ke Zaria ya bayyana wannan a Kano.

Malamin jami’ar yana cikin wadanda suka gabatar da jawabi na musamman domin tunawa da tafiyar NEPU wanda ta cika shekara 72 da kafuwa.

Shugaban jami’ar BUK, Farfesa Sagir Adamu Abbas, yace an zabi wannan rana ta yau ne domin a mai kamarta aka haifi jam’iyyar NEPU a shekarar 1950.

Jaridar Daily Trust tace an yi taron ne a dakin taro na Mambayya House, Kano a farkon makon nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng