Baiwa ce daga Allah: Hoton mata masu tsawon rai da kakar kakarsu ke da rai ya janyo cece-kuce

Baiwa ce daga Allah: Hoton mata masu tsawon rai da kakar kakarsu ke da rai ya janyo cece-kuce

  • A ranar Alhamis, 4 ga watan Augustan 2022, wani hoton jerin mata na zamani biyar daga dangi daya ya jijjiga kafafen sada zumuntar zamani
  • A hoton, akwai 'ya, mahaifiyarta, kakarta, mahaifiyar kakarta da kuma kakar karta duk a raye kuma cike da koshin lafiya
  • Legit.ng ta nemo daya daga cikin matan dake hoton nan inda ta bada sirrin irin wannan dadewa da karkon da suke yi a raye

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Busari Aderonke Abeke, mata mai shekaru 30 a duniya wacce ta kammala digirinta daga jami'ar fasaha ta Ladoke Akintola ta bayyana sirrin tsawon ransu wanda aka gani a hoton da ta dauka har da kakar kakarta.

A yayin da ta wallafa hoton a ranar 4 ga watan Augusta, bata taba tsammanin cewa zai yadu a kafafen sada zumuntar zamani ba kuma ya janyo hankulan jama'a zuwa ga danginsu.

Kara karanta wannan

Bidiyon Ango Ya Zurfafa Cikin Tunani Yayin Da Amaryarsa Ke Girgijewa A Wajen Liyafar Aurensu

Fifth Generation
Baiwa ce daga Allah: Hoton mata masu tsawon rai da kakar kakarsu ke da rai ya janyo cece-kuce. Hoto daga @IdeaTextile
Asali: Instagram

Hoton guda daya tilo ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta inda mutane da yawa ke son sanin sirrin doguwar rayuwarsu.

A yayin zantawa da Legit.ng, Abeke wacce ita ce ta biyu a karancin shekaru a hoton ta bayyana cewa dangin mahaifiyarta ne kuma sirrin wannan doguwar rayuwar kawai ikon Allah ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta kara da bayyana cewa, ana samun masu tsawon rai a dangin mahaifiyarta. Su 'yan asalin Iwo ne daga jihar Osun.

An gano wadanda ke cikin hoton

Kamar yadda Abeke tace, akwai Nasiratu Arike mai shekaru 95 wacce ta kasancewa tsohuwar cikin hoton. Ita ce ta haifa diya daya tal, Salawudeen Sikiratu Aduke mai shekaru 72 a duniya.

Aduke ita ce tsohuwa ta biyu a hoton kuma yara 8 gareta amma diyarta ta farko ita ce mai shekaru 55 mai suna Azeez Funmilayo Anike. Anike ce ta uku a hoton kuma ta haifa yara uku.

Kara karanta wannan

Sukar gwamnatin Buhari da tagwayen Indimi ke yi ya janyo cece-kuce

Babbar diyar Anike ce Busari Aderonke Abeke mai shekaru 30 a duniya wacce ita ce ta hudu a hoton. Da ita Legit.ng ta tattauna.

Abeke ce mahaifiyar yarinyar dake hoton wacce ke da suna Olatunji Tiwatope Abike mai shekaru 8 a duniya wacce ta bayyana ta biyar a hoton.

Bidiyo: An haska bidiyon Hajiya Dada, mahaifiyar Yaradua tana rera addu'o'i ga Yassine da Shehu a wurin liyafa

A wani labari na daban, bidiyon mahaifiyar marigayin tsohon shugaban kasar Najeriya, Alhaji Umaru Musa Yaradua, Hajiya Dada Yaradua, tana jero addu'o"in fatan zaman lafiya ga Shehu 'Yaradua da amaryarsa ya bayyana.

An haska wannan bidiyon ne a majigi yayin da ake tsaka da liyafar auren 'yan gatan, Yassine Sheriff da Shehu Yaradua.

Asali: Legit.ng

Online view pixel