Bidiyon Shigowar Kasaita Da Amarya Amina Isiyaka Rabiu Tayi A Wajen Liyafar Aurenta

Bidiyon Shigowar Kasaita Da Amarya Amina Isiyaka Rabiu Tayi A Wajen Liyafar Aurenta

  • Komai idan aka ce na manya ne ya kan zo da sabon salo da ba a saba gani ba, harma ka ga ya zama abun kwaikwayo a cikin mutane
  • Amina Isiyaka Rabiu ta yi wani kasaitaccen bayyana a wajen liyafar bikinta da angonta Muhammad Shehu Rabiu
  • A cikin bidiyon shahalin wanda tuni ya yadu a soshiyal midiya, an gano amaryar tafe a cikin wani abun daukar amare da aka kera don ita

Ana ta daure-dauren aure na ‘ya’yan manya a fadin kasar inda a wannan makon shagalin ya fada a kan yar mutan Kano.

A yanzu haka ana nan ana gudanar da shagulgulan bikin Amina Isiyaka Rabiu da angonta Muhammad Shehu Rabiu.

Tuni bidiyon kasaitaccen liyafa na musamman da aka shiryawa sabbin ma’auratan ya yadu a shafukan soshiyal midiya.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Amarya Ta Zage Ta Kwashi Garar Girki Kafin Ta Shiga Filin Rawa

Amarya
Bidiyon Shigowar Kasaita Da Amarya Amina Isiyaka Rabiu Tayi A Wajen Liyafar Aurenta Horo: surykmata
Asali: Instagram

A cikin wani bidiyo da shahararriyar MC nan ta Arewa wacce ake yayi a yanzu, Surrykmata ta wallafa a shafinta na Instagram, an gano lokacin da amarya Amina ta shigo dakin taron.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai sabanin yadda aka saba inda kawaye ke yiwa amarya rakiya, Amina ta shigo ne a cikin wani abun dauka yayin da wata tawaga ta musamman ke rike da abun.

An kuma gano amaryar a tsakiyar abun wanda aka kera shi kamar gida tana tafiyar kasaita zuwa wajen da aka tanada domin zamanta da angon nata.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

neelah_elegance ta ce:

"Ikon Allah"

mum_albanys_kitchenworld ta rubuta:

"Kai jamaaa anty barni in yi magana ana abu aduniya"

sumeebelels_cuisine ta ce:

"Tohm bakina alekum, nidei dan tambaya zan yi dama"

shopers_delight_kn ta ce:

Kara karanta wannan

Bidiyon Ango Ya Zurfafa Cikin Tunani Yayin Da Amaryarsa Ke Girgijewa A Wajen Liyafar Aurensu

"In da ranka ka sha kallo"

its_teamerh ta yi martani:

"Wannan shine namu ba irin nasu bane"

Zukekiyar Diyar Sarkin Kano, Ruqayya Aminu Bayero Za Ta Shiga Daga Ciki

A wani labarin kuma, mun ji cewa Ruqayya Aminu Bayero, kyakkyawar diyar sarkin Kano, Mai martaba Alhaji Aminu Ado Bayero, na shirin amarcewa da angonta.

Za a kulla aure tsakanin Rukayya da angonta Amir Kibiya a ranar Juma’a, 2 ga watan Satumba mai kamawa a fadar mai martaba Sarkin Kano.

Tuni katin gayyatar auren ya bayyana a shafukan soshiyal midiya kuma shafin fashionseriesng ya wallafa a Instagram.

Asali: Legit.ng

Online view pixel