Yajin aikin ASUU: Dalibin aji 2 a jami'a ya koma sayar da shayi a Kano
- Wani dalibin da ke zaman banza sakamakon yajin aiki malaman jami'a karkashin ASUU ya kama sana'a
- Yusuf Auwal Barkum na daya daga cikin dubban daliban Najeriya ke shan fama yayin yajin aikin ASUU
- Ya yi kira ga abokan karatunsa da su ma su duba su kama sana'ar da za ta kawar da hanlinsu daga zaman banza
Jihar Kano - Wani dalibin aji biyu na Jami’ar Yusuf Maitama Sule da yajin aiki ASUU ya shafa ya kama wata sana’ar sayar da “Shayi” a garin Dawakin Dakata da ke karamar hukumar Nassarawa ta jihar Kano domin kaucewa zaman banza.
Dalibin mai karanta Tarihi da Hulda da Kasashen Duniya wanda ya bayyana sunansa da Yusuf Auwal Barkum, a wata hira da ya yi da Sahelian Times, ya ce ya yi nadamar rashin kama sana’ar tun da farko.
Teburin shayi dai kasuwanci ne na gida inda ake sayar da dafaffiyar taliya, kwai, shayi da burodi, galibi a fili da ke da karamin shago da benci, teburi da kujeru a zagaye dasu.
A cewarsa:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Muna da majalisar muka saba zama muna tadi, da yawa daga cikinmu za mu sha shayi, kuma yawancin mashaya shayin sukan je wurare masu nisa don siya."
Barkum ya ce daga baya ne ya fahimci cewa zai iya bunkasa harkar kasuwancin shayi a kusa da wurin.
Ya kara da cewa:
"Na karbi rance daga dangi da abokai, na hada abin da ke hannu na, na fara aiki."
Dalibin da ya kama wannan sana’ar kimanin kwanaki 10 da suka gabata ya shaida wa jaridar cewa tuni ya fara danke ribarsa a hannu kuma a kwanan baya ya dauki ma’aikacin da zai ke taimaka masa.
A cewarsa:
“A yanzu da ke sana’ar na biyan bukatuna sai na dauki hayar wani da nake biyan Naira 300 a kowace rana, ba na dogara ga kowa wajen neman taimakon kudi.”
Dalibin ya shawarci takwarorinsa da ke ci gaba da zaman banza sakamakon yajin aiki ASUU da su kama sana'a kafin lokaci ya kure musu.
Daga shiga rubuta JAMB: An kama wani matashi da ya fece da wayoyi 21 da aka bashi ajiya
A wani labarin, jami’an tsaron NSCSC sun kama wani matashi dan shekara 23 mai suna Quadri Qudus wanda ake zargi da satar wayoyin hannu 21 daga masu neman shiga jami’a a Ilorin babban birnin jihar Kwara.
An zargi Quadri da satar wayoyin ne daga hannun masu neman shiga jami’a a lokacin da suke rubuta jarrabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandare a wata cibiyar jarrabawa kwamfuta da ke Ilorin a ranar 5 ga Yuli, 2022.
Sai dai kafin daliban su kammala rubuta jarrabawarsu, wanda ake zargin ya tsere daga cibiyar tare da wayoyin da aka ba shi ajiya.
Asali: Legit.ng