Abin Da Yasa Muka Kama Dan Takarar Gwamna Na Labour Party A Plateau, Yan Sanda

Abin Da Yasa Muka Kama Dan Takarar Gwamna Na Labour Party A Plateau, Yan Sanda

  • Rundunar yan sandan Najeriya reshen Jihar Plateau ta bayyana dalilin da yasa ta kama dan takarar gwamnan na jam'iyyar LP a jihar
  • Alabo Alfred, mai magana da yawun yan sandan Jihar Plateau ya ce wani abokin kasuwancin Amb, Yohanna Margif ne ya shigar da korafi kansa cewa ya bashi chekin kudi na bogi
  • Wannan dalilin ne yasa yan sanda suka gayyaci dan takarar gwamnan ya zo ya yi bayani, kuma ya gasgata abin ba wai dalilan siyasa ne yasa aka kama shi ba kamar yadda wasu rahotanni a dandalin sada zumunta ke cewa

Jihar Plateau - Rundunar yan sandan Najeriya reshen Jihar Plateau ta yi bayanin dalilin da yasa ta kama dan takarar gwamna na jam'iyyar Labour Party, LP, Ambasada Yohanna Margif, a jihar, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Har Yanzu Ni Dan Gani Kashe Nin Buhari Ne, In Ji Fasinjan Da Aka Ceto Daga Jirgin Kasar Kaduna Zuwa Abuja

Margif
Abin Da Yasa Muka Kama Dan Takarar Gwamna Na Labour Party A Plateau, Yan Sanda. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

A ranar Juma'a ne yan sanda dauke da makamai suka kama dan takarar na LP.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kakakin rundunar yan sandan, Alabo Alfred, cikin wata sanarwa ya ce an kama shi ne bayan korafin aikata laifi kan dan siyasan, ya kara da cewa ba siyasa bace ta saka aka kama shi kamar yadda ake yada wa a kafafen sada zumunta.

Ya ce:

"Akasin rahoton da ake yada wa a kafafen sada zumunta na cewa kama Ambasada Yohanna Margif da yan sandan Plateau suka yi na da alaka da siyasa, rundunar na son sanar da mutane cewa rahoton ba gaskiya bane kuma ba shi da tushe.
"Wani abokin kasuwancin Amb. Margif, wani E.C. Gajere ne ya shigar da korafin aikata laifi kansa inda ya yi ikirarin Amb. Margif ya bashi cheque ta bogi a wani kasuwanci da suka yi a baya-bayan nan. Don haka, muka gayyaci Amb. Margif ya amsa zargin da ake masa kuma ya gasgata hakan."

Kara karanta wannan

An Cafke Mutumin Da Ya Kai Yan Mata Otel, Ya Sace Musu iPhone 6 Bayan Zuba Musu Maganin Barci Cikin Abin Sha

Sanarwar ta kara da cewa:

"Rundunar yan sandan jihar Plateau tana son jadada cewa Rundunar Yan sanda hukuma ce wacce bata siyasa kuma tana bincike kan laifuka ba tare da la'akari da wanda abin ya shafa ba."

2023: Rikicin PDP Ya Dauki Sabon Salo, Gwamnoni Da Ke Goyon Bayan Wike Sun Gindayawa Atiku Sabbin Sharruda

A wani rahoton, gwamnonin jam'iyyar PDP da ke biyaya ga gwamnan Rivers, Nyesom Wike, sun bada wasu sharruda ga dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar, kafin su mara masa baya a zaben 2023, kamar yadda aka rahoto.

A cewar Daily Independent, gwamnonin za su hadu da Atiku a karshen mako don tattaunawa kan matsalolin da ke adabar jam'iyyar.

Jaridar ta rahoto cewa daya daga cikin mambobin tawagar Gwamna Wike yana cewa duk ma abin da ya faru, sun amince babu wanda zai fita daga jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel