2022: Kaduna da sauran jihohi 4 a Najeriya da suka fi ko ina runtumo rancen waje

2022: Kaduna da sauran jihohi 4 a Najeriya da suka fi ko ina runtumo rancen waje

  • Yayin da Naira ta rage daraja idan aka kwatanta da darajar dala saboda wasu dalilai, jihohin Najeriya ka iya shiga tasku
  • Ya zuwa watan Disamban 2021, basusukan waje na jihohi 36 kadai ya kai akalla dala biliyan 4.77, wanda gagarumin kari ne daga inda yake a shekarun baya
  • Jihohi biyar ne ke kan gaba a wannan bashi na ala-ka-kai da kaso mai tsoka, wanda jihar Legas ke gaba-gaba

Yayin da Naira take kara rugujewa idan aka kwatanta ta da dalar Amurka, biyan basussukan da ake bin jihohi 36 na Najeriya ya kara tsada.

Bayanai daga ofishin kula da basussuka (DMO) sun nuna cewa a watan Disamba 2021 jimillar basussukan waje na gwamnatocin jihohi 36 hade da babban birnin tarayya Abuja ya kai dala biliyan 4.77.

Kara karanta wannan

Ganduje zai cika alkawari, zai rattaba hannu domin rataye wanda ya kashe Hanifa

Jihohi 5 na Najeriya da suka fi tara bashin waje
2022: Kaduna da sauran jihohi 4 a Najeriya da suka fi ko ina runtumo rancen waje | Hoto: @sanwolu @wike @uzodima
Asali: Facebook

A lokacin da ake canjar dala 1 a matsayin N409.6 a watan Disamba 2021, basukan waje na jihohi ya kai Naira tiriliyan 1.9.

Da farashin canjin ya komai N428.12 kan dala 1 ya zuwa ranar Alhamis 4 ga watan Agustan 2022 bashin da ake bin jihohi ya kai Naira tiriliyan 2.4..

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jihohin da ke da mafi girman yawan bashi na kasashen waje

Ya zuwa watan Disamban 2021, jihohin da suka fi tara basussukan waje sun hada da Legas, Kaduna, Cross River, Edo, da Ribas.

Jihar Legas

Jihar Legas, cibiyar kasuwancin Najeriya, ta fi kowa yawan tara basussukan waje tun watan Disamban bara.

Ana bin jihar bashin dala biliyan 1.33 ya zuwa Disamban 2021, a hakan ma ya ragu daga dala biliyan 1.40 na Disamba 2020, a cewar bayanai daga Ofishin Kula da Bashi.

Kara karanta wannan

Ministan Harkan Noma Ya Ce Duk Da Matsalar Tsaro Abinci Bai Shafi Harkar Noma ba

Bashin jihar Legas a baya ya tashi zuwa dala biliyan 1.47 a watan Disamban 2017 daga dala biliyan 1.21 a watan Disamban 2015.

Jihar Kaduna

Jihar Kaduna ce ta biyu mafi yawan bashin waje tun daga watan Disamban 2021.

Bashin da ake bin Kaduna na waje ya karu zuwa dala miliyan 567.48 a karshen shekarar da ta gabata daga dala miliyan 554.78 a watan Disamban 2020 da kuma dala miliyan 222.88 a watan Disamban 2016.

Jihar Cross River

Jihar Cross River na da bashin waje na dala miliyan 279.7 ya zuwa watan Disamban 2021.

Bashin jihar na waje ya ragu zuwa dala miliyan 192.5 a watan Disamban 2020 daga dala miliyan 209 na watan Disambar 2019. Ya tsaya kan dala miliyan 115 a watan Disamban 2016.

Jihar Edo

Jihar Edo ta samu ragi a bashin da ake bin ta zuwa dala miliyan 276.3 na watan Disamban 2021 daga dala miliyan 280.3 a shekarar da ta gabace ta. Bashin jihar na kasashen waje ya tsaya akan dala miliyan 168.2 a watan Disamban 2015.

Kara karanta wannan

Majalisar Tarayya Ta Bayyana Abin da Zai Hana a Tunbuke Buhari Daga Karagar Mulki

Jihar Rivers

Jihar Rivers na da tarin bashin da ake bin ta da ya haura zuwa dala miliyan 147.8 a watan Disamban 2021 daga dala miliyan 96.7 a watan Disamban 2020.

Basusukan waje na jihar ya tsaya akan dala miliyan 46.9 a watan Disambar 2015.

2022: Burodi ke kan gaba a jerin abincin da ke son fin karfin talakan Najeriya

A wani labarin, karancin albashi da yadda hauhawar farashin kaya ke karuwa a kullum, yana da matukar wahala ka rayu a matsain talaka a Najeriya.

Ba wai kawai farashin abubuwa ba ne ke dagula lissafin talaka tare da gigita kwanciyar hankalinsa, akwai tunanin zuwa kasuwa tare da jin abin tsoro na yadda farashin ke kara shillawa sama.

Hukumar Kididdiga ta Kasa kwanan nan ta sanar da cewa hauhawar farashin abinci, wanda galibi ke kayyade ingancin rayuwar ‘yan kasa, ya karu zuwa 20.6% a watan Yunin 2022.

Kara karanta wannan

Sabbin Hotunan Gwamnan Jihar Neja Yana Tuka Babur Sun Bayyana

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.