Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Cewa Matsalar Tsaro Bai Shafi Al’amarin Noma Ba

Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Cewa Matsalar Tsaro Bai Shafi Al’amarin Noma Ba

  • Ministan noma, Mohammed Abubakar, ya ce duk da matsalar tsaro da ake fama da shi a kasar, abinci bai ragu ba
  • Mohammed Abubakar ya ce Bankin Raya Afrika (AfDB) ta amince da ba wa Najeriya tallafin dala miliyan 538 dan Inganta Noma
  • Ministan Harkan Noma na Najeriya ya ce Najeriya ce ta daya a nahiyar Afirka, kuma ta 4 a duniya wajen noman shinkafa

Abuja - Ministan noma, Mohammed Abubakar, a ranar Alhamis ya ce duk da kalubalen tsaro da ake fama da shi a kasar, abinci bai ragu ba. Rahoton Channels TV

Ministan ya amince da cewa rashin tsaro ya na hana manoma shiga gonakinsu, musamman a yankin Arewa wanda hakan abin damuwa ne ga gwamnatin tarayya.

Ya ce, duk da haka, ana ci gaba da samar da abinci a matakin da ya dace a wasu sassan yankunan kasar.

AGRIC
Gwamnatin Tarayya Ta Yi Ikrarin Cewa Matsalar Tsaro Bai Shafi Al’amarin Abinci Ba FOTO Channels TV
Asali: UGC

Ministan ya ci gaba da bayyana cewa, an samar da ayyuka kai tsaye daga kudin tallafin harkar noma na dala biliyan 1.1 da kasashen waje suka bada.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, Bankin Raya Afirka (AfDB) ta amince da ba da tallafin dala miliyan 538 domin a samar da shiyyoyin sarrafa noma na musamman a Najeriya.

Ya baiwa jihohin da suka halarci taron kamar su Akwa Ibom, Bauchi, Kano, Katsina, Kogi, Kwara, Kebbi, Ogun, Ondo, Oyo, Plateau da Sokoto.

Yayin da yake karyata rahotannin baya-bayan nan da ke cewa Najeriya ba ta kan hanyar kawo karshen yunwar abinci nan da shekarar 2025.

Abubakar ya bayar da misali da yadda Najeriya ke samar da wadataccen abinci wanda ya sanya kasar a matsayi na daya a nahiyar Afirka, kuma ta 4 a duniya wajen noman shinkafa.

Abubakar ya kara da cewa hakan na nuna cewa shugaba Muhammadu Buhari ne ke kan gaba wajen cika alkawarin da ya yi na fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci cikin shekaru goma.

Bayan Umarinin Buhari, Sojoji Za Su Gudanar Da Wani Atisaye Mai Taken ‘Operation Babu Tausayi'

A wani labari kuma, Hafsoshin jami’an tsaro sun fara aiwatar da umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari na dakatar da hare-hare da kashe-kashen da ‘yan ta’adda ke yi nan take. Rahoton LEADERSHIP

A jiya ne hafsoshin Rundunar sojoji suka kaddamar da wani Atisaye mai Taken “Operation Show No Mercy wato Nuna ‘Yan Ta’adda rashin Tausayi”.

Asali: Legit.ng

Online view pixel