NNPP: Bayan Janye Wa Kwankwaso, Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Ci Zaben Fidda Gwani Na Gwamna a Ogun

NNPP: Bayan Janye Wa Kwankwaso, Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Ci Zaben Fidda Gwani Na Gwamna a Ogun

  • Olufemi Ajadi Oguntayinbo, tsohon mai neman takarar tikitin shugaban kasa a NNPP ya zama ɗan takarar gwamnan jam'iyyar a Ogun
  • Hakan na zuwa ne bayan zaben raba gardama da aka gudanar a sakatariyar jam'iyyar bayan soke zaben da aka yi a baya tsakanin shugabannin bangarori biyu na jam'iyyar
  • Oguntayinbo, wanda dan kasuwa ne ya janye wa tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso domin ya zama ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar a zaben 2023

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ogun - Tsohon mai neman takarar shugabancin kasa na jam'iyyar NNPP, Olufemi Ajadi Oguntayinbo, ya zama ɗan takarar gwamna na jam'iyyar a Jihar Ogun.

Olufemi Ajadi Oguntayinbo
NNPP: Mutumin Da Ya Janye Wa Kwankwaso Takara Ya Ci Zaben Fidda Gwani Na Gwamna a Ogun. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Daily Trust ta gano cewa an yi zaben raba gardamar ne a Abeokuta bayan shugabannin jam'iyyar sun soke takarar yan takara biyu na bangarori biyu na jam'iyyar Ezekiel Fayoyin da Mrs Kassim Jackie-Adunni.

Kara karanta wannan

Rikicin siyasa: Tsigaggen mataimakin gwamnan PDP ya ja zuga, masoyansa sun koma APC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Oguntayinbo, dan kasuwa, da farko ya janye daga takarar shugabancin kasar jam'iyyar don bawa Rabi'u Musa Kwankwaso tsohon gwamnan jihar Kano daman zaman ɗan takarar shugabancin kasar.

Amma, daga baya ya zama ɗan takarar gwamna a zaben raba gardamar da aka sake yi na NNPP a sakatariyar jam'iyyar da ke Abeokuta.

A yayin da ya ke sanar da Oguntayinbo a matsayin wanda ya lashe zaben bayan kuri'ar murya da aka yi a sakatariyar jam'iyyar a Abeokuta, shugaban kwamitin zabe kuma baturen zaɓe na jam'iyyar, Abdullahi Tukur Dogonnama, ya ce abinda jam'iyyar ta yi ya dace da dokokin INEC na canja yan takara.

Martanin Oguntayinbo

A jawabinsa na godiyaz Oguntayinbo ya gode wa mambobin jam'iyyar da daligets saboda goyon baya da damar yi musu hidima.

Ya bayyana gamsuwarsa kan yadda aka gudanar da zaben, yana mai cewa ya yi murnar yadda aka yi zaben.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Sakateriyar PDP ta dagule, ana ta kira ga tsige shugaban jam'iyya

Martanin Shugaban jam'iyyar NNPP ta Ogun

Kwamared Olaposi Oginni, shugaban NNPP na Jihar Ogun yayin jawabi ga manema labarai bayan zaben fidda gwanin ya ce 'kuskure na ayyukan' ne ya janyo lamarin yana mai cewa zaben raba gardamar ya bawa jam'iyyar damar canja dan takarar gwamnanta.

Peter Obi Ko Tinubu? Afenifere Ta Bayyana Dan Takarar Shugaban Kasa Da Zata Goyi Baya a 2023, Ta Bada Dalili

A wani rahoton, Shugaban kungiyar Yarabawa ta Afenifere, Ayo Adebanjo, ya bayyana ainihin dalilin da yasa kungiyar ta ke goyon bayan Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na Labour Party.

Pa Adebanjo, ya bayyana cewa kungiyar na goyon Peter Obi na Labour Party don dakile cigaba da 'gazawar' gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, Premium Time ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164