Peter Obi Ko Tinubu? Afenifere Ta Bayyana Dan Takarar Shugaban Kasa Da Zata Goyi Baya a 2023, Ta Bada Dalili

Peter Obi Ko Tinubu? Afenifere Ta Bayyana Dan Takarar Shugaban Kasa Da Zata Goyi Baya a 2023, Ta Bada Dalili

  • Gabanin babban zaben shekarar 2023, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, yana cigaba da samun goyon baya daga mutane da fitattun kungiyoyi
  • A baya-bayan nan, kungiyar yarbawa ta Afenifere ta bayyana goyon bayanta ga Peter Obi, tsohon gwamnan Jihar Anambra
  • A wani rubutu da ya wallafa a Twitter a ranar Juma'a, shugaban kungiyar ya ce suna goyon bayan Obi a maimakon Tinubu domin tana son dakatar da cigaba da aikin da gwamnatin Buhari ta fara

Shugaban kungiyar Yarabawa ta Afenifere, Ayo Adebanjo, ya bayyana ainihin dalilin da yasa kungiyar ta ke goyon bayan Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na Labour Party.

Pa Adebanjo, ya bayyana cewa kungiyar na goyon Peter Obi na Labour Party don dakile cigaba da 'gazawar' gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, Premium Time ta rahoto.

Kara karanta wannan

Babbar matsala sabuwa ta kunno, Wasu Sanatocin APC sun goyi bayan tsige shugaba Buhari

Peter Obi, Tinubu da Pa Adebanjo.
Peter Obi Ko Tinubu? Afenifere Ta Bayyana Dan Takarar Shugaban Kasa Da Zata Goyi Baya a 2023, Ta Bada Dalili. Hoto: Peter Obi, Bola Tinubu, Afenifere group.
Asali: Facebook

Afenifere ta bada dalili

A wani sakon da ya wallafa a ranar Juma'a, 29 ga watan Yuli, Pa Adebanjo ya ce kungiyar bata goyon bayan Bola Tinubu, bayarabe, wanda shine dan takarar jam'iyyar APC mai mulki kuma tsohon gwamnan Jihar Legas, saboda zai cigaba da ayyukan gwamnati mai ci yanzu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rubutun na Twitter ta ce:

"Ahmed Tinubu kawai zai cigaba da gazawar gwamnatin Buhari. Mun san Peter Obi sosai, shi yasa muka goyi bayansa. Ba zai bawa yan Najeriya kunya ba, mu ajiye kabilanci a gefe mu zabi cancanta."

Kungiyar, tunda farko ta nuna goyon bayanta ga dan takarar shugaban kasa na Labour Party, Mr Obi, inyamuri kuma tsohon gwamnan Jihar Anambra, saboda lokaci na da ya kamata yan kudu su fitar da shugaban kasa.

Pa Adebanjo a wasu makonni ya ce:

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Mai Karfin Fada A Ji Ya Goyi Bayan A Tsige Buhari

"Eh, mun goyi bayan Peter Obi. Dalilin mu na goyon bayansa shine adalci da daidaito, ya kamata shugabancin kasa ya koma Kudu maso Gabas."

Sanata Daga Arewa Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Baya Goyon Bayan Tsige Buhari

A wani rahoton, shugaban kwamitin labarai da wayar da kan kasa na majalisar dattawa, Danladi Sankara ya nesanta kansa daga shirin da ake yi na tsige Shugaba Muhammadu Buhari, rahoton Daily Trust.

Sanata Sankara, wanda ke wakiltar Jigawa North West a Majalisar ya kuma nesanta kansa daga shirin tsige shugaban majalisa, Ahmad Lawan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel