Wata Jihar Arewa Ta Kwace Lasisin Dukkan Makarantun Frimare Da Sakandare Masu Zaman Kansu, An Bayyana Dalili
- Gwamnatin Jihar Plateau ta kwace lasisin dukkan makarantun frimare da sakandare masu zaman kansu a jihar
- Elizabeth Wampun, kwamishinan ilimin (sakandare) a jihar ne ta sanar da hakan yayin wani taron manema labarai a ranar Alhamis
- Wampun ta ce an dauki wannan matakin ne bayan an gano makarantun kudi fiye da 5000 a jihar suna aiki babu lasisi kuma ba su bin dokokin jihar
Jihar Plateau - Gwamnatin Jihar Plateau ta janye lasisin dukkan makarantun Nursery, Frimare da Sakandare masu zaman kansu a Jihar, Daily Trust ta rahoto.
Kwamishinan Ilimi na Jihar, Elizabeth Wampum, ce ta bayyana hakan yayin taron manema labarai a ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin janye lasisin makarantun masu zaman kansu
A cewar kwamishinan, an dauki matakin ne bayan an gano fiye da makarantu 5000 masu zaman kansu a jihar suna aiki babu lasisi.
Ta ce kashe 90 cikin 100 na makarantu masu zaman kansu a Plateau ba su bin dokokin gwamnati, ta kara da cewa kashi 85 cikin 100 na lasisin makarantu masu zaman kansu da aka bada a baya, sun lalace.
Ta ce:
"Ana sanar da dukkan mutanen cewa dukkan makarantun Nursery, Frimare da Karamar Sakandare da Babban Sakandare masu zaman kansu a Jihar sai sun sake sabunta lasisinsu."
Kwamishinan ta ce an dauki wannan matakin ne domin dakile bude makarantu ba bisa ka'ida ba barkatai da ake a jihar da kuma tallafawa wadanda ke bin dokoki, domin samun ilimi mai inganci ga kowa.
ASUU: Lakcarorin Jami'ar Kaduna Sun Bijirewa Umurnin El-Rufai, Sun Ki Zuwa Yi Wa Dalibai Jarrabawa
A wani rahoton, Kungiyar malaman jami'o'i ta Najeriya, ASUU, reshen Jami'ar Kaduna (KASU) ta ki komawa aji duk da barazanar da Gwamna Nasir El-Rufai ya yi na cewa zai kore su.
Mahukunta a makaranatar sun bukaci dalibai su dawo aji domin su cigaba da jarrabawansu bayan barazanar da gwamnan ya yi.
A ranar Litinin, an ga wasu daliban a aji suna rubuta jarrabawa inda shugaban jami'ar da wasu malamai ke duba su.
Asali: Legit.ng