Bayan Gwamnan Neja, Wani Gwamna A Arewa Shima Ya Haramta Karuwanci A Jiharsa
- Yahaya Bello, gwamnan Jihar Kogi ya bada umurnin a rufe dukkan gidajen karuwai da ke jihar baki daya
- Gwamna Bello ya kuma sanya dokar hana amfani da takunkumin fuska a wuraren taruwar al'umma don a rika gane fuskokin kowa
- Gwamnan ya kuma yi taro da shugabannin ƙananan hukumomi, jami'a tsaro, masu sarautar gargajiya da kungiyoyi don inganta tsaro a jihar
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jihar Kogi - Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bada umurnin a rufe dukkan gidajen da karuwai ke zama a jihar.
Ya kuma haramta saka takunkumin fuska a wuraren da al'umma ke taruwa saboda a rika gane kowa a jihar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Hakan ya biyo bayan wasu matsalolin tsaro ne da aka samu a jihar a baya-bayan nan, The Punch ta rahoto.
Ya bada umurnin ne a ranar Talata a Lokoja yayin wani taro da aka yi da sarakuna masu sanda mai daraja ta ɗaya da biyu da ma shugabannin ƙananan hukumomi.
Bello ya kuma bada umarnin rushe wasu kanguna a Lokoja, Osara, Zango, Itobe, Obajana da dukkan sassan jihar.
Ya umurci kwamishinan kananan hukumomi da masarautu, shugabannin ƙananan hukumomi, shugabannin kungiyoyi da jami'an tsaro su gana da masu adaidaita sahu don tantance su da daukan bayanan su.
Gwamnan ya kuma bukaci masu sarautun gargajiya su tsare garuruwansu su kuma tabbatar an tsefe dukkan lunguna da saƙuna.
"Tabbatar da zama lafiya a yankunan ku aikin ku ne. Nauyi ya rataya a kanku ku kawar da dukkan laifuka a yankunan da ke karkashin ku," in ji gwamnan.
Ya kuma mika ta'aziyya ga iyalan jami'an tsaro da aka kashe a karamar hukumar Ajaojuta a ranar Asabar da ta gabata.
Gwamnatin Neja Za Ta Haramta Karuwanci, Wasu Mata Da Ke Harkar Sun Magantu
Tunda farko, kun ji cewa gwamnatin Jihar Neja za ta haramta karuwanci a Minna babban birnin jihar a matsayin wani mataki na magance rashin tsaro, Daily Nigerian ta rahoto.
Kaltum Rufai, Sakataren dindindin a ma'aikatar mata da ayyukan cigaba na jihar ce ta bayyana hakan cikin wata hira da kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN, a Minna.
Ms Rufai ta ce gwamnati ta san da wannan lamarin mara dadi wanda ka iya zuzuta kallubalen tsaro da ake fama da shi a jihar.
Asali: Legit.ng