2023: Tinubu bashi da hannu a halin da gwamnatin Buhari ke ciki, Oshiomhole

2023: Tinubu bashi da hannu a halin da gwamnatin Buhari ke ciki, Oshiomhole

  • Tsohon shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomhole, yace Tinubu bashi da alhakin makomar mulkin shugaban Muhammadu Buhari
  • Kamar yadda ya bayyana, Tinubu bai taba rike wani mukamin siyasa a karkashin mulkin Buhari ba, don haka bai dace a zarge shi da komai ba
  • Ya bayyana cewa, yana daga cikin wadanda suka gina APC tare da Fashola da wasu gwamnoni, amma rashin adalci ne a zargesu kan makomar mulkinta

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Adams Oshiomhole, tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, ya bayyana cewa, 'dan takarar kujerar shugabancin kasa na jam'iyyar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ba shi da alhakin sakamakon mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Tsohon gwamnan jihar Edo din ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin tattaunawa da Arise TV, inda ya bayyana cewa Tinubu bai taba rike wani mukamin siyasa ba a mulkin Buhari.

Kara karanta wannan

Elrufai Ya Ce APC ta Riga Ta Nada Darakata Janar Na Kamfen Din Takarar Tinubu Da Shettima

Adams
2023: Tinubu bashi da hannu a halin da gwamnatin Buhari ke ciki, Oshiomhole. Hoto daga Independent.ng
Asali: UGC
Yace, "Ba zaka ce wanda bai taba rike wani mulki a gwamnati ba yana da alhakin makomar tsarikan gwamnatin ko kuma wata gazawa ta gwamnatin.
"Ina tunanin idan za a caccaka ko yabi mutane, ana duba rawar da suka taka ne. Tabbas Asiwaju da kansa yace da shi aka gina APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Nima tare da ni aka gina APC, Fashola da sauran gwamnoni amma bai taba shiga gwamnatin ba. Bai taba rike wani mukami ba. Bai taba karbar wata kwangila ba a madadin gwamnati, toh ta yaya za a alakanta shi da wani abu? Wannan ba adalci bane."

Allah ya bada sa’a: Fitaccen Farfesa Yana Goyon Bayan Tsige Buhari da Gwamnoni

A wani labari na daban, a ranar Talata, 3 ga watan Agusta 2022, Farfesa Wole Soyinka ya nuna goyon bayansa ga yunkurin majalisa na tsige Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Tsintsiya ta tsinke a Borno: Dan a mutun Tinubu ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

Jaridar Punch tace shahararren Farfesan wanda ya taba lashe kyautar Nobel laureate ta Duniya ya nuna goyon bayansa ne a Abeokuta, a jihar Ogun.

Da yake jawabi a bikin da aka yi domin murnar cikar Abeokuta Club shekara 50 a Duniya, Soyinka ya tabo batun tsige shugaba a tsarin farar hula.

Asali: Legit.ng

Online view pixel