Yan Bindiga Sun Sace Tsohon Dan Majalisar Najeriya A Gidansa

Yan Bindiga Sun Sace Tsohon Dan Majalisar Najeriya A Gidansa

  • Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace tsohon dan majalisar jihar Anambra, Benson Nwawulu daga gidansa
  • Rundunar yan sandan Jihar Anambra ta bakin kakakinta Tochukwu Ikenga ta tabbatar da sace Nwawulu amma ta ce ta aiki don ceto shi
  • Mr Nwawulu ya bar kujerarsa a majalisar tun a shekarar 2019, ya sake yin takara don ya koma amma bai yi nasara ba

Jihar Anambra - Yan bindiga a karamar hukumar Ihiala na Jihar Anambra sun sace tsohon dan majalisar dokokin jiha, Benson Nwawulu, The Punch ta rahoto.

Nwawulu dan majalisar dokokin jiha ne wanda ya yi wa'adi biyu a majalisar dokokin jihar Anambra.

Taswirar Jihar Anambra.
Yan Bindiga Sun Sace Tsohon Dan Majalisar Jihar Anambra. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun harbi shugaban 'yan sanda, sun kashe jami'in kariyarsa

Tun bayan barin kujeransa a shekarar 2019, ya sake yin takara amma bai yi nasara ba.

A cewar majiyoyi, an sace shi ne a gidansa da ke Ihiala a ranar Lahadi.

Duk da cewa ba a bayyana bayanai wa al'umma batun sace shin ba, majiyoyi sun ce dan sa ya tuntubi wasu yan majalisar jihar domin su taimaka masa da kudi.

Martanin yan sanda

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Najeriya a jihar, Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da sace shin, yana mai cewa an yi nisa a kokarin ceto shi.

Ikenga ya ce:

"Eh, an sace shi a ranar Lahadi, kuma muna aiki domin ganin an sako shi.
"Za a ceto shi nan ba da dadewa ba, saboda muna bin sahunsu, kuma munyi nisa sosai, nan bada dadewa ba za a ceto shi."

'Ni Na Rika Yi Wa Yan Bindiga Magani,' Fasinjar Jirgin Kaduna Da Ya Samu Yanci Ya Magantu

Kara karanta wannan

Allah ya bada sa’a: Fitaccen Farfesa Yana Goyon Bayan Tsige Buhari da Gwamnoni

A wani rahoton, Mustapha Imam, daya daga cikin mutanen da yan bindiga suka sace jirgin kasar Kaduna zuwa Abuja ya ce ya yi wa yan bindiga magani a lokacin da ya ke tsare a hannunsu.

A wani bidiyon da Tukur Mamu, mawallafin Desert Herald wanda ya taimaka wurin tattaunawa don ganin an sake su, fasinjan ya bayyana zamansa a hannun yan bindigan a matsayin 'lamari matukar muni'.

Imam, wanda ma'aikaci ne a jami'ar Usman Danfodiyo da ke Sokoto, ya ce ba zai yi wa makiyinsa fatan shiga halin da ya tsinci kansa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel